Gwamnatin jahar jigawa ta kara karfafa hulda da IITA don habbaka harkar noma afadin jahar
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla haɗin gwiwa da Cibiyar Binciken Noma ta Duniya (IITA) a wani bangare na ƙudirin Gwamna Malam Umar Namadi na sauya fasalin harkar noma a jihar.
Wannan ya biyo bayan wata babbar tawaga daga cibiyar, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Darakta Janar na IITA, Mista Abdoulaye Tahirou, wanda ya wakilci Darakta Janar, a ziyarar girmamawa da suka kai Fadar Gwamnati a birnin Dutse, kamar yadda Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Hamisu Muhammad Gumel, ya bayyana.
Tawagar ta nuna matuƙar godiya ga Gwamnatin Jihar Jigawa bisa kyakkyawar tarba da aka yi musu. Jawabin Mista Tahiru ya nuna gamsuwa da kuma cikakken goyon baya, tare da jaddada cewa akwai manufa guda da ɓangarorin biyu ke son cimmawa.
Mista Tahiru ya bayyana cewa tawagar ta yi tattaunawa mai zurfi da jami’an gwamnatin Jigawa, wanda ya haifar da shirin sauya fasalin noma mai tsari, a taƙaice kuma mai sauƙin aiwatarwa, wanda aka tsara bisa bukatun jihar
“Mun shirya tsaf, a matsayin abokan hulɗa na fasaha, mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Mai Girma Gwamna da al’ummar Jigawa domin aiwatar da wannan shiri.”
Ya ƙara da cewa tawagar ta ƙunshi kwarraru a fannin haɓaka iri, abinci mai gina jiki, kimiyyar ƙasa, tsarin samar da iri, da muhimman amfanin gona da ake nomawa a jihar.
Daga bisani, ya roƙi gwamnatin jihar da ta halatta filin ƙasar da IITA ke amfani da shi tun kusan shekaru 25 don ayyukan bincike, yana mai cewa yin hakan a hukumance zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar.
Da yake mayar da martani, Gwamna Malam Umar Namadi ya bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci kuma ta zo a kan kari, musamman bayan ziyarar da gwamnatin jihar ta kai hedikwatar IITA kwanan nan.
Gwamnan ya tuna yadda ya yaba da manyan gine-gine da ƙwararrun ma’aikata na IITA, yana mai cewa cibiyar na da ƙwarewar da za ta iya sauya fasalin noma ba a Jigawa kaɗai ba, har ma a faɗin Najeriya.