Dawowar gwamnan kano abba kabir yusuf APC zai haifar da da mai ido -commarade Rabiu Abubakar Tunfafi
Sakataren Kungiyar kasuwar Abinci ta Duniya Dawanau dake karamar hukumar Dawakin Tofa kuma fitaccen Dansiyasa anan jihar Kano Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi, ya bayyana cewar dawowar Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf zuwa jamiyyar APC abune da zai haifar da ‘da’ mai ido a fadin jihar Nan.
Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi yace, idon aka yi duba da abubuwan da Gwamnan ya zayyana suka sanya shi ya sauya sheka akwai bukatar Kara hada kan alummar jihar Kano guri guda,ta yadda zai samu damar ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa da tallafawa alumma da Samar da cikakken zaman lafiya Mai dorewa.
Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi jamiyyar APC tana jagoranci nagari da shugabanni tun tun daga kananan hukumomi har zuwa matakin kasa.Sakataren yace injiniya Abba Kabir Yusuf mutune jajirtacce Wanda yana Yi masa cikakken zato wajen gudanar da jagoranci nagari a tsakanin ‘ya’yan jamiyyar APC daya tarar da Wadanda suka biyo shi zuwa jamiyyar APC.
Shugaban yace akwai bukatar alummar jihar Kano su kwantar da hankulansu wajen hada Kai tsakanin juna, musamman yadda lokacin zaben shekarar 2027 dake tafe.
Sakataren Kungiyar kasuwar Abinci ta Duniya dake Dawanau yace, a matsayinsa na Dansiyasa Kuma Dankasuwa ya bayyana cewar zai ci gaba da baiwa Shugabancin jamiyyar APC tun daga jihar har yanzu tarayya, Wanda Hakan zai taimaka gaya wajen bunkasa rayuwar Alummar Najeriya.
Haka zalika yayi kira ga ‘ya’yan jamiyyar APC da su jajirtacce wajen hada kansu ta yadda za”a tafiyar da shugabancin da zai taimaki magoya bayan alumma a fadin kasar Nan.
Kwamared Rabiu ya Kuma sha alwashin tallafawa kungiyar kasuwarsa ta Dawanau domin bunkasa kasuwancin jama’ar da suke aiwatar da kasuwanci, musamman kananan yankasuwa domin su samu damar tsayawa da kafafuwansu kamar sauran jama’a.
Tumfafi ya bukaci Gwamnatoci a matakai daban daban musamman Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancinsa Gwamnan injiniya Abba Kabir Yusuf daya taimakawa alumma da suke kasuwanci a cikin jihar Kano, Inda Kuma ya godewa Gwamnan Kano bisa ziyarar da ya kasuwar singa tare da ba da tallafin kudade miliyan dari domin rage masu radadi sakamakon iftilain gabarar suka yi.
Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi ya jajantawa alummar da suka gamu da wannan iftilain gabarar tare da yin fatan Allah subahanahu wata’ala ya mayar musu da alkhairi bisa Asarar da suka yi ta miliyoyin kudade.
Daga karshe ya yi kira ga alummar kasuwar Abinci ta Duniya dake Dawanau, da su saukawa alumma, musamman yadda watan Azimin Rama dana yake karatowa.