Uwar gidan tsohon shugaban kasa Aisha Buhari da ƴaƴanta sun ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku a Saudiyya

Mai ɗakin tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari ta ziyarci jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar.

 

 

 

Cikin wani saƙo da Atikun ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce Aisha Buhari ta tare da ƴarta Hanan Buhari da wasu ƴan’uwanta sun ziyarce shi a masaukinsa da ke Saudiyya.

 

 

 

”Kamar dai ni, mai ɗakin tsohon shugaban ƙasar, da iyalanta na ƙasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umara”, kamar yadda saƙon Atikun ya bayyana.

 

 

 

Tun bayan mutuwar mijinta a watan Yulin 2025, Aisha Buhari ta fara takaba a garin Daura da ke jihar Katsina, kafin daga baya ta koma Kaduna, inda ta kammala a can.

You might also like
Leave a comment