Gwamna Makinde Yabada umarnin Takaita Ayyukan Okada a Jihar Oyo
Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde, ya sanya hannu kan Dokar Zartarwa mai lamba 002 ta shekarar 2026 domin ƙarfafa tsaro, tabbatar da bin dokokin rajistar ababen hawa da kuma inganta tsarin kula da zirga-zirga a jihar.
Matakin ya biyo bayan karuwar matsalolin tsaro, musamman sace malamai da dalibai a karamar hukumar Oriire.
A yayin bikin sanya hannu kan dokar a ofishinsa da ke Ibadan, Makinde ya bayyana cewa dokar za ta ba hukumomin da abin ya shafa damar aiwatar da dokokin rajistar ababen hawa da na zirga-zirga ba tare da sassauci ba.
Ya nuna damuwa kan yadda ake amfani da motoci, babura da adaidaita sahu marasa rajista wajen aikata laifuka, yana mai cewa rashin bayanan rajista kan jawo cikas ga binciken jami’an tsaro.
A cewarsa, dokar ta bai wa jami’an da aka ba izini damar kama masu karya doka tare da kwace motocinsu, baburansu ko adaidaita sahunsu idan aka same su suna aiki ba bisa ka’ida ba.
Takaita Ayyukan Okada
Daya daga cikin muhimman abubuwan da dokar ta kunsa shi ne sanya takunkumi kan ayyukan masu baburan haya (okada) a fadin jihar.
Sabuwar dokar ta haramta wa masu sana’ar okada gudanar da aiki tsakanin karfe 10:30 na dare zuwa 5:30 na safe a kowace rana.
Gwamnan ya ce an dauki wannan mataki ne domin rage ayyukan miyagu, kara sa ido da kuma inganta tsaron jama’a.
Makinde ya bayyana damuwarsa kan yadda malamai da daliban da aka sace a Oriire suka shafe sama da kwanaki 20 suna hannun masu garkuwa da mutane.
Yace “Muna cikin mawuyacin lokaci. Malamanmu da dalibanmu sun shafe fiye da kwanaki 20 a hannun ‘yan ta’adda. Muna ci gaba da tunawa da su da iyalansu cikin addu’a.”
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa na ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin ganin an kubutar da wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Gwamnan ya bukaci mazauna jihar da su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani motsi ko aiki da ke tayar da hankali.
yace. “Idan ka ga wani abu mai tayar da hankali, ka sanar da hukuma, kuma hukumomi za su dauki mataki.”
Haka kuma ya bukaci jama’a su yi amfani da layin gaggawa na jihar mai lamba 615 wajen kai rahoton duk wata barazana ga tsaro cikin gaggawa.
A ƙarshe, Makinde ya yaba wa jami’an tsaro da kuma jami’an Amotekun Corps bisa kokarinsu wajen yaki da matsalolin tsaro, yana mai nuna fatan cewa hadin gwiwar gwamnati, jami’an tsaro da al’umma za ta taimaka wajen ceto daliban da malaman da aka sace da kuma kara inganta tsaro a jihar Oyo.