Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji Tara a Wani Sansanin Soji a Borno
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari kan wani sansanin soji da ke Mandara-Girau a karamar hukumar Biu, inda suka kashe sojoji tara tare da jikkata wasu da dama.
Mandara-Girau na da nisan kilomita kadan daga garin Biu a jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun kai harin ne da sanyin safiyar Juma’a yayin da ake fama da ruwan sama mai karfi. An ce sun zo da yawa kuma suka bude wa dakarun sojin wuta ba tare da sun yi tsammani ba.
Wata majiya ta bayyana cewa harin ya yi sanadin asarar rayukan sojoji tara, yayin da wasu da dama suka samu raunuka. Haka kuma, an ce maharan sun mamaye wani bangare na sansanin sojin bayan artabun.
Rahotanni sun nuna cewa wani faifan bidiyo mai tsawon minti daya da dakika 38 ya nuna gawawwakin sojoji takwas da aka lullube da bargo a kasa.
Ya zuwa yanzu, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Wannan hari na daga cikin hare-haren da kungiyoyin masu tayar da kayar baya ke ci gaba da kai wa jami’an tsaro da al’ummomin yankin Arewa maso Gabas, duk da kokarin hukumomi na dakile ayyukansu.
Daily trust