Kotu Ta Dakatar da Shari’ar Neman Cire Rajistar ADC da Sauran Jam’iyyu

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar da ke neman a soke rajistar jam’iyyun siyasa da suka hada da African Democratic Congress (ADC), Accord Party da Action Alliance ba tare da sanya sabon ranar ci gaba da sauraron karar ba.

 

 

 

 

 

Mai shari’a, Peter Lifu, ya sanya ranar Juma’a domin yanke hukunci a karar da kungiyar Incorporated Trustees of the National Forum of Former Legislators ta shigar kan wasu jam’iyyun siyasa.

 

 

 

 

 

Sai dai sauraron karar ya tsaya bayan Accord Party ta samu umarnin dakatar da shari’ar daga Kotun Daukaka Kara a ranar 29 ga Mayu.

 

 

 

 

 

A lokacin zaman kotun, magatakardar kotun ta sanar da bangarorin da ke shari’ar cewa an dage yanke hukuncin, kuma za a sanar da sabon rana a gaba.

 

 

 

 

 

 

 

Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaban kwamitin amintattu na National Forum of Former Legislators, Raphael Igbokwe, ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin da Kotun Daukaka Kara ta dauka na dakatar da ci gaba da shari’ar.

 

 

 

 

 

 

Ya ce kungiyar ta riga ta daukaka kara zuwa Kotun Koli domin kalubalantar wannan hukunci.

 

 

 

 

 

A cewarsa:  “Mun damu ganin cewa shari’ar da ta kai matakin yanke hukunci yanzu ta tsay  a sakamakon umarnin dakatar da shari’a. A zahiri, wannan yana nufin dakatar da yanke hukunci.”

 

 

 

 

 

 

Ya kara da cewa duk da hakan, kungiyar za ta ci gaba da bin duk hanyoyin da doka ta tanada domin tabbatar da an warware batutuwan da ke cikin karar, domin karfafa dimokuradiyya da bunkasa dokokin kundin tsarin mulki da na zabe a Najeriya.

 

 

 

 

 

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026 ta sanya Independent National Electoral Commission (INEC) a matsayin wanda ake kara na farko.

 

 

 

 

 

Sauran wadanda aka hada a karar sun hada da jam’iyyun siyasa kamar ADC, AA, Action Peoples Party (APP), Accord Party da Zenith Labour Party da wasu jam’iyyu.

 

 

 

 

 

 

Masu karar sun yi zargin cewa wadannan jam’iyyu ba su cika sharuddan kundin tsarin mulki da suka shafi samun goyon bayan masu zabe a fadin kasa da kuma nasarorin zabuka ba.

 

 

 

 

 

 

Sun kuma yi ikirarin cewa doka ta tanadi cewa jam’iyyun siyasa su samu akalla kashi 25 cikin 100 na kuri’u a zabukan da aka kayyade domin ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyu masu rijista.

 

 

 

 

Saboda haka, sun bukaci kotu ta bayar da umarnin soke rajistar wadannan jam’iyyu, suna masu cewa wadanda ake kara ba su gabatar da hujjojin da za su rusa wannan ikirari ba. (NAN)

You might also like
Leave a comment