Majalisar Dattawa Ta Amince da Dokar Hukumar Yaki da Kawar da Zazzabin Cizon Sauro ta Kasa,

Kungiyar Maternal Accountability Mechanism in Kaduna Initiative (KADMAM) ta yabawa Majalisar Dattawan Najeriya bisa amincewa da kudirin dokar kafa Hukumar Yaki da Kawar da Zazzabin Cizon Sauro ta Kasa (National Malaria Elimination Agency), tana mai bayyana matakin a matsayin gagarumin ci gaba wajen karfafa yaki da cutar zazzabin cizon sauro da inganta lafiyar al’umma, musamman mata da yara.

 

 

 

 

A cikin wata sanarwa da Garba Muhammad, Shugaban KADMAM na hadin gwiwa, ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna, kungiyar ta ce kudirin dokar wani muhimmin mataki ne na rage yawan matsalar zazzabin cizon sauro a Najeriya.

 

 

Sanarwar ta ce  “Zazzabin cizon sauro na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara a Najeriya, tare da jefa iyalai da al’ummomi cikin mawuyacin hali.”

 

 

 

 

 

 

KADMAM ta bayyana cewa kafa wata hukuma ta musamman da za ta mayar da hankali wajen kawar da cutar zai samar da damar kara inganta shirye-shiryen rigakafi da magani, da kuma hanzarta cimma burin kawar da zazzabin cizon sauro a fadin kasar nan.

 

 

 

 

 

Kungiyar ta ce amincewar da Majalisar Dattawa ta yi da kudirin dokar ya samo asali ne daga kokarin wayar da kai da hadin gwiwar ‘yan majalisa, masu rajin kare lafiya, kungiyoyin fararen hula, abokan hulda na ci gaba, kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki.

 

 

 

 

Ta kuma yaba da gudunmawar da KADMAM, Kaduna Health Advocacy Media Alliance (KADHAMA) da sauran kungiyoyin kafafen yada labarai suka bayar wajen tallafa wa wannan yunkuri da kuma kara karfafa kiraye-kirayen samar da ingantattun tsare-tsare na yaki da zazzabin cizon sauro.

 

 

 

 

KADMAM ta kuma yaba wa masu daukar nauyin kudirin dokar, mambobin Majalisar Tarayya da dukkan masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen ganin an cimma wannan nasara ta doka.

 

 

 

 

 

Har ila yau, kungiyar ta yi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya gaggauta sanya hannu kan kudirin domin hanzarta kafa hukumar da kuma kara karfin martanin Najeriya ga daya daga cikin manyan kalubalen lafiyar jama’a.

 

 

 

 

Duk da murnar wannan nasara, KADMAM ta jaddada cewa nasarar hukumar idan an kafa ta za ta dogara ne kan kyakkyawan aiwatarwa, gaskiya, rikon amana da kuma ci gaba da nuna kudurin siyasa a kowane mataki.

 

 

 

 

Kungiyar ta kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar an samar wa hukumar isassun kudade, ma’aikata da kayan aikin fasaha domin ta iya sauke nauyin da aka dora mata yadda ya kamata.

 

 

 

 

 

 

 

A karshe, KADMAM ta tabbatar da shirinta na ci gaba da hada kai da hukumomin gwamnati, abokan hulda na ci gaba, kungiyoyin fararen hula, kafafen yada labarai da shugabannin al’umma wajen tallafawa wayar da kai, sa ido da kuma hada kan jama’a domin cimma burin kawar da zazzabin cizon sauro a Najeriya.

You might also like
Leave a comment