Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Abubakar Matawalle, ya gargadi masu amfani da kafafen sada zumunta da su ji tsoron Allah wajen yaɗa sashihan labarai musamman waɗanda suka shafi aikin Hajjin.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Abubakar Matawalle, ya gargadi masu amfani da kafafen sada zumunta da su ji tsoron Allah wajen yaɗa bayanai, musamman waɗanda suka shafi aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki.

 

 

 

 

 

 

Alhaji Ibrahim Matawalle ya yi wannan kira ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ƙasa mai tsarki, inda ya nuna damuwa kan yadda wasu ke yaɗa bayanan da ba a tantance ba ko kuma marasa inganci ba tare da tabbatar da gaskiyarsu ba.

 

 

 

 

 

Ya ce bai dace ba a rika yaɗa bayanai a matsayin labarai ba tare da cikakken bincike da tantancewa ba, domin hakan na iya jawo ruɗani da tashin hankali ga alhazai da iyalansu da ke Najeriya.

 

 

 

 

Daraktan Janar ɗin ya ƙara da cewa alhazan Jihar Kano na gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hankali, yayin da jami’an hukumar ke ba su cikakken kulawa da goyon baya domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.

 

 

 

 

 

 

A ƙarshe, Alhaji Ibrahim Abubakar Matawalle ya buƙaci alhazai da su kasance masu haƙuri da juriya a duk tsawon lokacin aikin Hajji, tare da mayar da hankali kan ibadunsu domin samun yardar Allah da albarkarsa.

You might also like
Leave a comment