Mataimakin shugaban kasa Shettima zai wakilci Tinubu bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Benin

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya tafi birnin Cotonou domin wakiltar Bola Tinubu a bikin rantsar da sabon shugaban jamhuriyar Benin, Romuald Wadagni.

 

 

 

 

 

Shettima ya bar Najeriya a yau Asabar daga birnin tarayya Abuja, inda zai halarci bikin da zai gudana a gobe Lahadi a fadar shugaban Benin.

 

 

 

 

 

 

 

Tsohon Ministan Kuɗin na Benin ya yi nasara ne da gagarumin rinjaye a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 12 ga watan Afrilu, inda ya samu fiye da kashi 94 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

 

 

← Back

Thank you for your response. ✨

 

 

You might also like
Leave a comment