Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina tayi nasarar cafke wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane tare da kwato kudi da makamai
Rundunar ‘Yan sandan sun bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne ta hanyar wani samame na musamman da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri ƙarƙashin sabuwar sashen yaƙi da manyan laifuka mai suna Violent Crime Response Unit (VCRU).
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ya ce an sace yaron ne ranar 13 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma yayin da yake dawowa gida daga makarantar Islamiyya.
Sanarwar ta ce washegari bayan sace yaron, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa inda suka nemi kuɗin fansa har Naira miliyan 50 kafin su sake shi.
Bayan tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu, iyalan yaron sun biya Naira miliyan 17 kafin aka sako shi.
Da samun rahoton lamarin, jami’an ‘yan sanda suka fara bincike cikin gaggawa, inda a ranar Juma’a suka samu nasarar cafke mutum shida daga cikin ƙungiyar.
‘Yan sanda sun bayyana sunayen waɗanda aka kama da:
Nura Aliyu mai shekaru 39, wanda aka bayyana a matsayin jagoran ƙungiyar kuma maƙwabcin iyalan yaron;
Abubakar Aminu, mai shekaru 37;
Ibrahim Muhammad, mai shekaru 51;
Iliyasu Sani, mai shekaru 51;
Abubakar Muhammad, mai shekaru 27;
Abdullahi Isma’il, mai shekaru 30.
A yayin bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu tare da bayyana cewa akwai wani abokin aikinsu mai suna Abdul wanda har yanzu bai shiga hannu ba.
Rundunar ta ce tuni aka fara farautar wanda ya tsere domin Kamashi.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da mota kirar Peugeot 307, babur kirar Boxer, da kuma Naira miliyan 7.5 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansar da aka karɓa, tare da wasu kayayyaki daban.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Katsina, Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa gaggawa da nasarar da suka samu, yana mai jaddada aniyar rundunar na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a jihar.