Yan jam,iyyar APC a Kano Sun Saya Wa Gwamna Abba Kabir Yusuf Fom ɗin Takara

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano sun sayi fom ɗin nuna sha’awa   tsayawa takara (expression of interest and nomination forms) domin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

 

 

 

 

 

 

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ne ya miƙa fom ɗin ga gwamnan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Alhamis.

 

 

 

 

 

 

Miƙa fom ɗin ga gwamnan na nuni da yadda jam’iyyar ta amince da shi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam,iyyar  APC a Kano.

 

 

 

 

 

 

 

Haka kuma , masu ruwa da tsakin sun amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya tilo na jam’iyyar.

 

 

 

 

 

 

Sai dai shugabannin jam’iyyar sun bayyana cewa ba za a ba sauran masu neman takara tikitin kai-tsaye ba.

 

 

 

 

 

 

Sun ce duk sauran muƙaman siyasa za a tantance su ne ta hanyar tsarin cikin gida na jam’iyyar, musamman ta hanyar cimma matsaya.

 

 

 

 

 

Da yake miƙa fom ɗin ga gwamnan, Ganduje ya ce shugabannin jam’iyyar sun amince da Gwamna Yusuf domin ya sake neman wa’adi na biyu.

 

 

 

 

 

Ya ce, “Mun riga mun yarda cewa kai ne ɗan takarar gwamna guda ɗaya tilo. Don tabbatar da wannan alkawari, ni a matsayina na tsohon Mataimakin Gwamna na tsawon shekara takwas, tsohon Gwamna na tsawon shekara takwas, kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, ina miƙa maka waɗannan muhimman fom guda biyu.”

 

 

 

 

 

 

 

Ganduje ya bayyana cewa fom ɗin sun haɗa da na nuna sha’awa da na tsayawa takara, waɗanda dole ne a cike su tare da miƙa su kamar yadda dokokin jam’iyyar suka tanada.

 

 

 

 

 

 

A gefe guda kuma, Rabiu Sulaiman Bichi ne ya gabatar da kudirin amincewa da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, inda dukkan mahalarta taron suka mara masa baya.

 

 

 

 

 

 

Da yake jawabi tun da farko, Shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce tun farko jam’iyyar ta shirya sayen fom domin Tinubu a matsayin nuna goyon baya.

 

 

 

 

 

 

Ya ce, “Mun so mu sayi fom ɗin Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga Kano, amma sai muka ga wasu sun riga sun saya kafin mu. Duk da haka, hakan bai rage mana goyon baya ba.”

You might also like
Leave a comment