Hukumar NDLEA ta kama Ting Hung Kiong yar asalin kasar china bisa zargin shigo da kilogram 31 na wani nau’in tabar wiwi mai ƙarfi da ake kira “Canadian Loud” a filin jirgin saman Murtala Muhammed International Airport da ke Lagos.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA), ta kama wata tsohuwa ‘yar ƙasar China mai shekara 63 mai suna Ting Hung Kiong bisa zargin shigo da kilogram 31 na wani nau’in tabar wiwi mai ƙarfi da ake kira “Canadian Loud” ta filin jirgin saman Murtala Muhammed International Airport da ke Lagos.

 

 

 

 

 

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kama matar ne ranar Lahadi 17 ga Mayu, 2026 bayan ta iso daga Thailand ta bi ta Dubai cikin jirgin Emirates Airline.

 

 

 

 

A cewarsa, jami’an NDLEA sun gano manyan akwatuna guda biyu dauke da miyagun ƙwayoyin yayin bincike a sashen masu shigowa na Terminal 2.

 

 

 

 

 

Matar ta bayyana cewa tana aiki a matsayin mai kula da marasa lafiya a Malaysia, kuma ‘yarta ce ta dauki nauyin tafiyarta daga Malaysia zuwa Thailand sannan zuwa Najeriya. Ta kuma ce an ba ta kayan ne a filin jirgin Thailand domin ta kawo su Najeriya.

 

 

 

 

 

 

 

Hakazalika, NDLEA ta sanar da cafke wani babban kaya na magungunan opioid a sashen kaya na filin jirgin Lagos. Kayan, wanda ya fito daga India cikin jirgin Emirates Cargo, ya kunshi kwayoyi 1,825,710 na Tapentadol 250mg da kudinsu ya kai sama da naira biliyan 2.1.

 

 

 

 

 

 

A wani samame daban a filin jirgin saman Akanu Ibiam International Airport, jami’ai sun kama wani mutum mai suna Onyeka Valentine Emeka wanda ya fito daga Sierra Leone ta Addis Ababa. An ce ya fitar da gram 185.36 na hodar iblis (cocaine) daga cikinsa bayan an tsare shi domin bincike.

 

 

 

 

 

 

Haka kuma a Nnamdi Azikiwe International Airport, an kama wani injiniyan gine-gine mai shekaru 29 mai suna Babatunde Prosper Afekhide yayin da yake kokarin tafiya Milan, Italy. An gano kwayoyin Tramadol da Tapentadol sama da 10,000 a cikin jakarsa.

 

 

NDLEA ta kuma kama:

Kwayoyi 1,174 na Ecstasy da aka boye cikin kayan keken hawa da ake shirin kaiwa Netherlands.

 

 

 

 

Kwayoyin Tramadol da aka boye cikin kwalin sabulu da cream zuwa Amurka da Birtaniya.

 

 

 

Kilogram 489 na skunk da iri kilogram 9 a jihar Edo.

 

 

Kwayoyi 196,000 na Exol-5 daga hannun wani mai suna Isah Sani a hanyar Zaria zuwa Kano.

 

 

 

Kilogram 1,116 na skunk a wani sito a Ikole-Ekiti tare da kama Ogundana Adebayo Julius.

 

 

 

Shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya yabawa jami’an hukumar tare da bukatar su ci gaba da yaki da miyagun ƙwayoyi a fadin ƙasar nan.

You might also like
Leave a comment