Yan sanda sun kama mutum 3 kan kisan gilla da aka yi wa wasu mutane biyu a Bauchi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gilla da wasu mutane suka yi wa maza biyu a garin Bunga, da ke Karamar Hukumar Warji a jihar.

 

 

 

 

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Nafiu Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 7 ga Mayu, 2026.

 

 

 

 

 

 

Ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 11:50 na safe, dangane da wani hari da wasu mutane suka kai a Bunga Hamlet, Dagu Ward, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Kabiru Idris (mai shekara 30) da kuma Ibrahim Samaila Danliti (mai shekara 40), dukkansu daga kauyen Gabanga a Karamar Hukumar Warji.

 

 

 

 

 

A cewarsa, wadanda aka kashe suna kan babur ne lokacin da wasu mutane daga Karamar Hukumar Ningi suka rika binsu suna ihu da cewa “barayi, barayi”, kafin su tare su a Bunga Hamlet, inda suka yi musu duka mai tsanani.

 

 

 

 

 

 

 

“Jami’an ‘yan sanda sun garzaya da su zuwa Babban Asibitin Warji, amma likita ya tabbatar da cewa sun rasu,” in ji shi.
Sanarwar ta ce jami’an bincike, bisa bayanan sirri, sun kama mutane uku da aka bayyana sunayensu kamar haka:
Samaila Turawa daga Gwada
Danbaba Haruna daga Gwada
Ubale Mai Kaji daga Ningi

 

 

 

 

 

 

An ce ana zargin su da hannu a harin.
A halin yanzu, wadanda ake zargin suna tsare a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) a Bauchi, kuma suna taimakawa wajen bincike. Rundunar ta ce ana ci gaba da kokarin kamo sauran ‘yan kungiyar da suka tsere.

 

 

 

 

 

 

Kakakin rundunar ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Sani Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da kisan, tare da bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

 

 

 

 

An kuma ruwaito kwamishinan yana jaddada cewa:
“Babu wani mutum ko kungiya da ke da ikon kwace rayuwar wani ba bisa ka’ida ba.”

 

 

 

 

 

SP Nafiu Abubakar ya kara da cewa an dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da rundunar ta kara yawan sintiri da tuntubar al’umma domin hana sake faruwar irin wannan lamari.

 

 

“Rundunar za ta tabbatar da cewa an gano duk wadanda suka shiga wannan haramtaccen aiki tare da gurfanar da su gaban shari’a bisa doka,” in ji shi.

You might also like
Leave a comment