Ningi ya caccaki Oshiomhole da Akpabio kan rikicin sauya dokokin Majalisar Dattawa
Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ahmed Ningi, ya shiga cikin cece-ku-cen da ke kara ta’azzara game da gyaran Dokokin Tsayuwar Majalisar Dattawa (Senate Standing Rules).
Ningi ya bayyana rikicin da ke faruwa tsakanin sanatoci a matsayin “son kai” da kuma abin da ya samo asali daga burin neman mukaman shugabanci.
Sanatan, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Wasanni na Majalisar Dattawa, ya ce duka bangaren da ke goyon bayan gyaran dokar da kuma wadanda ke adawa da ita, suna yin hakan ne saboda amfanin kansu, ba wai saboda kishin kasa ko kare martabar Majalisar Dattawa ba.
Da yake magana a lokacin da ake ta cece-ku-ce kan sabon sharadin cancantar samun mukaman shugabanci a Majalisar, Ningi ya zargi wasu sanatoci da yin shiru a baya kan muhimman batutuwan kasa, amma yanzu suka fara magana ne saboda wannan sauyin dokar na iya shafar burinsu.
“Wannan son kai ne kuma abin da ya shafi kansu daga masu gabatarwa da masu adawa da shi,” in ji Ningi
Ya kara da cewa a lokacin da suka taba tasowa a zauren Majalisar domin nuna damuwa kan wasu sassan Dokar Zabe (Electoral Act), mutane da dama sun yi shiru saboda abin da ya kira tsoron bin umarnin jam’iyya.
“Amma yanzu da wasu suna ganin suna da burin neman mukami nan gaba, sai suka ga za a iya taba su,”
Ningi ya ce wannan rikicin ba ya da alaka da Najeriya kai tsaye, sai dai yana da alaka da Majalisar Dattawa da kuma masu neman shugabanci.
sannan ya tuna yadda aka kaddamar da Majalisar Dattawa ta 10 a 2023, inda ya ce an yi watsi da tsarin ranking (wato fifita wadanda suka dade a Majalisa wajen mukamai).
A cewarsa, an bai wa wasu sanatoci masu shiga Majalisar karo na farko manyan mukamai da kujerun shugabancin manyan kwamitoci duk da rashin kwarewar majalisa.
“A 2023 da muka shigo, an jefar da tsarin ranking,” in ji shi.
Ningi ya kuma yi zargin cewa wasu shugabannin kwamitoci sun gaza gudanar da aikinsu, inda ya ce wasu kwamitoci ba sa yin taro tun bayan kafuwar Majalisar, sai dai lokacin da aka kawo batun kasafin kudi.
“Akwai kwamitoci da shugabanninsu ba su taba kiran taro ba tun daga farko, sai dai lokacin kasafin kudi,
Sanatan ya ce cece-kucen da ake yi kan gyaran dokar Majalisar ya nuna yadda ake yawan tsara dokoki da matakai domin anfani da wasu mutane ko kungiyoyi a siyasa.
Rikicin ya biyo bayan wata zazzafar muhawara da ta faru tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Sanata Adams Oshiomhole, yayin zaman Majalisar kan gyaran dokokin.
Sabon gyaran dokar ya tanadi cewa sai sanatan da ya yi wa’adi biyu a jere (terms biyu) ne kawai zai iya tsayawa takarar mukaman Shugaban Majalisar Dattawa, Mataimakin Shugaban Majalisa, da sauran manyan mukaman shugabanci.
An amince da gyaran dokar ne bayan wani zaman sirri da ya dauki kusan awa uku, lamarin da ya haddasa rarrabuwar kai a Majalisar.
Masu sukar dokar sun ce an yi ta ne domin hana sanatoci masu wa’adi daya damar tsayawa takara a nan gaba.
Rahotanni sun ce rikicin ya kara kamari ne saboda rade-radin siyasa cewa Akpabio da Oshiomhole na iya shirin fafatawa kan kujerar shugaban Majalisar a gaba.