Rundunar ‘Yan Sandan jahar Zamfara Ta Samu Gagarumar Nasara A Yaki Da Laifuka
Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara Ta Samu Gagarumar Nasara A Yaki Da Laifuka
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta samu manyan nasarori wajen dakile laifuka a fadin jihar, cikin kasa da mako guda bayan sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ahmad Muhammad Bello, ya kama aiki.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau, Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce wadannan nasarori na daga cikin sabon shirin da rundunar ta bullo da shi domin kawar da masu aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
DSP Yazid ya tabbatar da cafke wani mutum mai suna Audu Maikano, wanda rundunar ta bayyana a matsayin jagoran wata kungiyar ‘yan bindiga da ke addabar jama’a a Karamar Hukumar Kaura Namoda.
Ya ce an kwato kayayyaki masu hatsari daga hannunsa, ciki har da:
Bindigar AK-47 da aka kera ta hannu
Harsasai guda 10 masu rai
Bindigogi kirar gida guda 14
Bindigar pistol
Adduna da takubba
Kayan Tsafe-tsafe
Wayoyi da dama
Ya kuma kara da cewa kungiyar tana addabar jama’a musamman a hanyoyin karkara tsakanin Kaura Namoda da Kasuwar Daji.
A wani samame kuma, rundunar ta kama wasu mutane biyu, Abdullahi Idris da Ibrahim Harisu, inda aka same su da buhuna biyu na busassun ganye da ake zargin tabar wiwi ce.
Haka zalika, rundunar ta kai farmaki wani maboyar masu safarar kwayoyi a Gusau, inda ta kwato:
Kwalaben “Shutter” guda 73
Robar rubber solution guda 116
Kwalaben codeine babu komai
Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin gano tare da kama sauran wadanda ke da hannu a lamarin.
DSP Yazid ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama mutane uku da ake zargi da tuki cikin ganganci da tayar da hankalin jama’a, wadanda ake danganta su da kungiyar “Yan Arlit.”
Inda yace an kwato:
Babura guda 9
Tabar wiwi
Bututun shan “ice”
Wuƙaƙe da sauran makamai
Ya ce an dauki matakin ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda kungiyar ke addabar al’umma.
A wani aiki daban, rundunar ta kama Wakala Ladan da Sharhabilu Wakala, bayan zargin su da kai wa mutane hari da adduna da sanduna.
Rundunar ta ce ta kuma kwato wani keke napep da aka sace, bayan kama Salisu Usman da Abu Abubakar Ishaka.
Hakazalika, rundunar ta kama wasu mutane uku da aka same su da mabuɗan babura guda 22, inda suka amsa cewa suna satar babura a jihohin Zamfara da Katsina.
DSP Yazid Abubakar ya nuna godiya ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Olutunji Rilwan Disu, da kuma gwamnatin jihar Zamfara bisa goyon bayan da suke bayarwa.
Ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa hadin kai da bayar da sahihan bayanai, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da daukar duk matakan doka domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.