Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bisa dalilin rikice-rikicen cikin gida da ke ƙara tsananta, tare da buƙatar kare babbar muradin al’ummar Jihar Kano.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.
A cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Mazabar Diso–Chiranchi ta NNPP a Karamar Hukumar Gwale, gwamnan ya sanar da hukuncinsa na ficewa daga jam’iyyar, wanda zai fara aiki daga Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.
“Ina rubuto wannan wasiƙa ne cikin cikakken godiya domin sanar da shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) cewa na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar, kuma wannan zai fara aiki daga Lahadi, 25 ga Janairu, 2026.”
Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu a tsawon lokacin da yake tare da NNPP.
“Ina matuƙar godiya ga damar da jam’iyyar, shugabanninta da mambobinta a faɗin Jihar Kano suka ba ni tun daga shekarar 2022, da kuma goyon baya, fatan alheri da haɗin kai da aka nuna mini a tsawon lokacin da nake cikin jam’iyyar.”