Yan majalissar tarayya bangaren marasa rinjiye sun tabbatar da anyi sauye sauye a dokar haraji ba bisa ka,idaba

Bangaren marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ya tabbatar da an yi sauye sauye ba bisa ƙa’ida ba a wasu dokokin haraji na ƙasar, ciki har da Sabuwar dokar haraji ta, 2025, bayan da Majalisar ta amince da su kuma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu.

 

Binciken kwamitin da Victor Ogene ke jagoranta ya nuna cewa an canza wasu tanade tanade da suka shafi haraji, ciki har da tilas ajiye kashi 20 na harajin da ake kalubalantar sa kafin a daukaka kara, da kuma bai wa jami’an haraji damar kama mutane ko sayar da kadarori ba tare da kotu ba. Haka zalika, wasu sassa sun cire harajin mai da na VAT yayin da wasu suka tilasta amfani da dala maimakon kudin Najeriya kamar yadda aka tsara.

 

Kwamitin ya ce wannan bincike ya nuna bukatar zurfafa nazari kan dokokin haraji, inda aka nemi karin lokaci domin tabbatar da gaskiya. Bangaren yan majalisar ya gode wa shugabannin rukunin saboda amincewa da su kan wannan aiki, wanda ke da nufin kare ikon Majalisar da tabbatar da bin tsarin dimokuradiyya.

You might also like
Leave a comment