Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde,ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya ce ya kai ziyarar ne domin tattaunawa da shugaban kasa kan “wasu batutuwan da suka shafi mulki” ba na siyasa ba.
Ganawar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauye a siyasance, gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.
A baya bayan dai wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka haɗa da gwamnoni suka fice daga jam’iyyar zuwa APC, inda suka bar Makinde da wasu tsiraru a jam’iyyar ta adawa.
Da aka tambaye shi ko zai koma APC nan ba da jimawa ba, Makinde ya jadada cewa hankalinsa a kwance ya ke a PDP.
Ya ce ”Hankali na a kwance ya ke a PDP. Waɗansu abubiuwa na iya tasowa a ƙasar nan ida ke buƙatar a yi watsi da batun ɓangaranci, inda ba zai zama batun wataƙila APC ta yi magana ita kaɗai ko PDP ta yi magana ita kaɗai ba.”
Ya yi nuni da cewa, yayin da shi da Shugaban ƙasar ke jam’iyyun siyasa daban-daban, ci gaban Najeriya ya kasance wani aiki ne da ya kamata duka ƴan kasa su damu da shi ba tare da la’akari da ra’ayin siyasa ba.