An Kama ’Yan Najeriya 11 a kasar thailand Kan Zargin Damfarar soyyaya

Hukumomin shige da fice da ’yan sanda a Thailand sun kama ’yan Najeriya 11 bayan tarwatsa wata kungiyar damfarar soyayya ta kasa da kasa da ke aiki a yankin Muang Thong Thani.
Wata kafar yada labarai ta cikin gida, Thailand News, ta ruwaito  cewa ana zargin kungiyar da yin damfarar soyayya ta intanet, inda suke yaudarar mata ta kafafen sada zumunta.
Binciken ya fara ne bayan wata ’yar Thailand ta kai kara a shekarar 2025, tana cewa wani mutum da ta hadu da shi a Facebook kuma suke soyayya da shi ya damfare ta.
Rahoton ya ce mutumin ya bayyana kansa a matsayin wani injiniyan kasar China mai suna “Bingwen Fu”, sannan ya shawo kan matar ta tura masa fiye da baht miliyan biyu zuwa wani asusun banki na bogi, da hujjar cewa kudin za a yi amfani da shi ne wajen aikin gini.
’Yan sanda sun bi diddigin kudaden da aka tura, inda suka gano cewa lamarin na da alaka da wata babbar kungiya ta damfara da ke amfani da mutane daban-daban wajen rike asusun karbar kudi.
Bincike ya nuna cewa kungiyar tana aiki ne daga wani gini (condominium) a jihar Nonthaburi, inda kowane mutum ke da rawar da yake takawa, kamar:
masu damfara ta intanet,
masu cire kudi,
da masu nemo asusun banki (account recruiters).
Bayan samun bayanan sirri, Kwamishinan Hukumar Shige da Fice, Pol Lt Gen Phanumas Boonyaluck, ya bayar da umarnin kai farmaki tare da hadin gwiwar ’yan sanda, inda aka tarar da wadanda ake zargi suna tsaka da yin damfarar soyayya kai tsaye ta wayoyi da kwamfutoci.
A yayin samamen, wasu daga cikin wadanda ake zargi sun yi yunkurin tserewa ba takalmi, amma jami’an tsaro suka kama su.
Hukumomi sun tabbatar da cewa:
mutane 8 sun wuce wa’adin bizarsu (visa overstay),
yayin da ’yan Najeriya 5 suka shiga Thailand ta haramtacciyar hanya ta iyakar Laos.
Dukkan wadanda aka kama yanzu suna fuskantar tuhume-tuhume na:
wuce wa’adin biza,
da shiga kasa ba bisa ka’ida ba.
’Yan sanda sun kwace na’urori 34 da suka hada da:
kwamfutoci (laptops),
da wayoyin hannu,
inda aka samu shaidu na damfarar hadin gwiwa ta hanyar kwaikwayon attajirai daga kasashen Turai da Asiya domin yaudarar mata ’yan Thailand da na kasashen waje.
Haka kuma, masu bincike sun gano alaka da wani shari’a a Nong Khai, da kuma shaidu cewa ana tura kudaden zuwa Najeriya ta hanyar kudin dijital (cryptocurrency).
Rahoton ya ce ’yan sanda na ci gaba da bincike domin rushe sauran sassan kungiyar da kuma gano karin masu hannu a ciki.
Wannan kamen ya zo ne jim kadan bayan kama wani dan Najeriya a Thailand bisa zargin laifin miyagun kwayoyi.
Rahotanni a baya sun ce wani dan Najeriya mai suna Ukoma Jefta Nuzbech, wanda ke zaune a Thailand, an kama shi bayan da ya tsere daga shari’ar da ake yi masa kan safarar kwayoyi a yankin Koh Pha Ngan.

You might also like
Leave a comment