Dakarun rundunar hadin gwuiwa na operations hadin kai sungano wani Kato kabari da aka bunne gawarwakin yan ta,adda kusan 20 a yanki Timbuktu jahar barno
Dakarun hadin gwiwa na Operation HADIN KAI sun gano wani katon kabari da ke dauke da gawarwakin kusan ’yan ta’adda 20 a yankin Timbuktu Triangle na jihar Borno. Gawarwakin na daga cikin ’yan ta’addan da aka kashe yayin hare-haren soji a yankin.
An bayyana gano kabarin ne a ranar Laraba, kamar yadda jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya sanar. Ya bayyana cewa gano kabarin na kara nuna yadda hare-haren soji ke janyo asarar rayuka mai yawa a cikin kungiyoyin ’yan ta’adda a yankin.
Laftanar Kanal Sani Uba ya ce sojoji ne suka kashe ’yan ta’addan a yayin artabu, yayin da sauran abokan aikinsu da suka tsere suka binne gawarwakin daga baya. Rundunar ta jaddada ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda domin dawo da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Gabas.