Shugaban kasa bola Ahmad tunibu ya amince da tura jakadun nigeria 4 zuwa kasashen waje
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura jakadu huɗu daga cikin mutum 68 da Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da su a watan Disambar da ya gabata.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun Fadar Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya tabbatar da naɗa Ambasada Ayodele Oke a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar Faransa, yayin da Kanal Lateef Are zai kasance jakadan Nigeria a kasar Amurka.
Haka kuma, shugaban ya amince da naɗa Ambasada Aminu Dalhatu, tsohon jakadan Najeriya a Koriya ta Kudu, a matsayin jakadan Najeriya a Birtaniya.
Sanarwar ta kuma ce Usman Isa Dakingari Suleiman, tsohon gwamnan jihar Kebbi, shi ne jakadan Najeriya a ƙasar Turkiyya. Wannan na zuwa ne yayin da ake sa ran Shugaba Tinubu zai kai ziyarar aiki zuwa Turkiyya a mako mai zuwa.
A wata takarda da ya aikawa Ma’aikatar Harkokin Waje, Shugaba Tinubu ya umarci ma’aikatar da ta sanar da gwamnatocin ƙasashen huɗun game da naɗin jakadun, kamar yadda ƙa’idojin diflomasiyya suka tanada.