Gwamnatin Anambra ta soke umarnin zaman gida ranar Litinin

Gwamnatin jihar Anambra ta sanar da dakatar da batun zaman gida a ranar Litinin a jihar “cikin gaggawa”.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakatariyar hukumar kula da ilimi nma matakin farko ta jiha Mgbemena Loveline E, a madadin hukumar.

 

Haka kuma   ta yi gargaɗin cewa ma’aikatan gwamnati, waɗanda suka bi umurnin zama a gida za su gani a kwarya a lokacin biyan albashi.

 

“Wannan umarnin na nufin, duk wani ma’aikaci, mai koyarwa a aji ko mara koyarwa, wanda ya kasa zuwa makaranta ko ofis a ranar Litinin, ko dai zai karbi kashi 20 na albashinsa ko kuma ya yi asararsa baki daya,” in ji sanarwar.

 

Manyan sassan jihar Anambra sun kwashe shekaru da dama suna gudanar da zaman gida na mako-mako a kowace ranar Litinin – lamarin da ke dakatar da harkokin kasuwanci da zamantakewa a faɗin jihar.

 

Tun farko dai ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a yankin kudu maso gabashin ƙasar ne suka kafa wannan dokar, lamarin dai ya haifar da fargaba da rashin son gudanar da harkokin kasuwanci a tsakanin mazauna yankin, inda kasuwanni da makarantu da wuraren aiki suka kasance a garƙame a farkon kowanne mako.

 

Ana kallon wannan umarnin na zama a gida a matsayin mai cutarwa ga rayuwar al’umma da kuma tattalin arzikin.

You might also like
Leave a comment