Gwamnatin Tarayya ta gina Gidaje sama da dari da sauran ababan more rayuwa kamar yadda tayi alkawari a garin Tudun Biri

Gwamnatin Tarayya ta gina Gidaje sama da dari da tituna tareda magudanar ruwa da Asibiti da sauran ababan more rayuwa a garin Tudun Biri kamar yadda tayi alkawari.

 

Shugaban Hulɗa da jama,a na hukumar  Alhaji Nuhu Abdullahi shine ya bayyana hakan lokacin taron bayyana ayyukan Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da akeyi a yanki Arewacin Najeriya kashi na hudu da aka gabatar a Kano.

Yace Gwamnatin tarayya yanzu haka tana aikin gina hanyar Minna zuwa Zungeru zuwa Tagina zuwa Kontagora da kuma aikin hanyar Dukko Junction zuwa Minna duk a Jihar Niger.

Alhaji Nuhu Abdullahi ya kara da cewa aikin hanyar da akayi watsi dashi shekara da shekaru wanda ya tashi daga Adamawa zuwa Fufure ya hade da kan iyakar Camaroon da Najeriya tuni an kusa kammalashi a wannan Gwamnati ta shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A bangaren Lafiya kuwa Gwamnatin tarayya  ta inganta tare da fadada Asibitin Sir Patrick Yakowa a jihar Kaduna da fadada Asibitin Koyarwa na Moddibo Adama dake Birnin Yola a jihar Adamawa.

A bangaren Ilimi kuwa Shugaba Tinubu ya mayar da Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya dake Zaria zuwa Jami’a tareda kokarin samar da Jami’ar Kimiyya dake Kachia duk a jihar Kaduna

You might also like
Leave a comment