Shettima ya Tashi daga Nigeria zuwa ƙasar Switzerland Domin halastar babban taron tattalin arziki na duniya

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja domin halartar babban taron tattalin arziki na duniya karo na 56 da ake gudanarwa a kowace shekara a Davos, ƙasar Switzerland.

Kafin halartar babban taron, Shettima zai fara da wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da sabon Shugaban Ƙasar Guinea-Conakry, Mamadi Doumbouya, bayan nasarar da ya samu a zaɓe.

An shirya bikin rantsarwar ne a ranar Asabar, 17 ga Janairu, a filin wasa na GLC Stadium da ke Nongo, a birnin Conakry.

Halartar mataimakin shugaban ƙasar a bikin rantsarwar na da muhimmanci wajen ƙarfafa jagorancin Najeriya a yankin, da bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki bisa manufar Tinubu na sabunta fata.

 

Wannan mataki na cikin rawar da Najeriya ke takawa a matsayin jagaba a ƙungiyar ECOWAS, musamman wajen tallafa wa Guinea domin komawa kan tafarkin mulkin farar hula bayan shafe shekaru huɗu tana ƙarƙashin mulkin riƙon ƙwarya.

Daga Guinea, mataimakin shugaban ƙasar zai wuce zuwa Davos-Klosters a Switzerland domin halartar babban taron tattalin arziki na duniya, wanda za a gudanar daga ranar 19 zuwa 23 ga Janairu, 2026.

 

A yayin taron na Davos, Shettima zai gana da shugabannin duniya da masu zuba jari domin tattauna manufar sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya da damar zuba jari a ƙasar, da kuma rawar da Afirka za ta taka wajen gina makomar tattalin arzikin duniya mai ɗorewa da haɗin kai.

 

Ana sa ran Shettima zai koma Najeriya bayan kammala dukkan ayyukansa a taron na Davos.

You might also like
Leave a comment