Yan Majalisar Rivers sun buƙaci kotu da ta binciki shirin tsige Fubara
Majalisar dokokin jihar Rivers ta buƙaci babban alƙalin jihar ya kafa kwamitin bincike kan zargin aikata manyan laifuffuka da ake yi wa gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu.
‘Yan majalisar sun ɗauki matakin ne a ranar Juma’a bayan zaman da suka yi a Fatakwal, babban birnin jihar, tare jaddada aniyarsu ta ci gaba da shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa daga muƙamansu.
Da yake jawabi a zaman, Shugaban masu rinjaye na majalisar kuma wakilin mazaɓar Akuku-Toru ta daya, Major Jack, ya ce dalilin ci gaba da shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa shi ne yadda suka ci gaba da saɓa wa ƙundin tsarin mulki tare da nuna rashin girmamawa ga majalisar dokoki.
Ya ce duk da shiga tsakani da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, gwamnan da mataimakiyarsa ba su mayar da martani kan sanarwar tsigesu da za a yi da aka miƙa musu ba, kuma ba su ɗauki wani mataki ba domin kare kansu daga zarge-zargen da aka yi musu.
Major Jack ya buƙaci kakakin Majalisar da ya ba da damar ci gaba da shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa wanda ya saka majalisar ta yanke shawarar kiran ɓabban alƙalin jihar da ya kafa kwamitin bincike domin yin bincike a kansu da zargin da ake musu.