Jami’an Ƴan Sanda Sun 3 Kama Dodanni U A Akwa Ibom

Rundunar ƴan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama dodanni uku da ake zargi da tayar da tarzoma da tsoratar da jama’a a karkashin guise ɗin al’adun dodanni.

Kakakin ƴan sandan jihar, Timfon John, ya shaida wa manema labarai a Uyo ranar Asabar cewa an kama dodannin ne a ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Etinan.
Ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 4:45 na Rana rundunar ta samu kiran gaggawa daga wani da ba a san ko wanene ba, cewa wasu dodanni suna tayar da tarzoma a ƙauyen Mbioto II, Etinan LGA,” in ji Kakakin.

Bayan haka, jami’an ƴan sanda sun gaggauta zuwa wurin, inda suka kama dodanni biyu da shugabansu. Wadanda ake zargi sun hada da: Kenneth Bassey (31), Ofonime Isaac (25), da Paul Samuel Bassey (21).

An kama wadanda ake zargi, kuma suna bada hadinkai ga  jami’an ƴan sanda wajen bincike,” in ji Kakakin.

A baya, Gwamnan jihar, Umo Eno, ya sanya hannu kan wata dokar umarni a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2025, wacce ta haramta duk wani abu da dodanni ke yi na tsoratar da jama’a. Rundunar ƴan sanda ta dauki mataki wajen kama da gurfanar da wasu dodanni a lokacin bukukuwan.

You might also like
Leave a comment