Rundunar Sojojin kasarnan sun kama wata mata da ake zargin tana kai wa ƴan Boko Haram tabar wiwi
Dakarun rundunar hadin guiwa ta arewa maso gabas, Operation HADIN KAI, sun kama wata mata mai shekaru 65 da haihuwa, bisa zarginta da safarar miyagun ƙwayoyi ga ƴan ƙungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a sassan jihar Borno.
Wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar ta ce an kama wanda ake zargin ne a karamar hukumar Askira uba da ke jihar Borno, a ranar 23 ga watan Junairu, 2026, yayin wani samame da rundunar ta kai sakamakon bayanan sirri da ta tattara.
Sanarwar ta ƙara da cewa ana zargin matar ne da zama babbar mai samar da tabar wiwi ga ƴan Boko Haram da ke aiki a faɗin yankin da ya haɗa da Askira Uba da Rumirgo da Gwahi da Wamdiyo, da Uvu da kuma Gaya.
Binciken farko dai ya nuna cewa wadda ake zargin ta samo tabar wiwin ne daga ƙaramar hukumar Sarti Baruwa ta jihar Taraba kuma an kama ta da ƙunshin ganyen wiwi guda 14 mai nauyin kimanin kilogiram 30.
”A halin yanzu dai wadda ake zargin ta na tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, don ganowa tare da wargaza hanyoyin da ake amfani da su wajen safara da rarraba miyagun ƙwayoyin”. In ji sanarwar