Jam’iyyar APC ta zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na jiha domin jagorantar harkokin jam’iyyar a jahar Kano.

An gudanar da zaben ne a daren Talata, inda aka zabi Umar Haruna Doguwa a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar na Jiha. Doguwa ya yi murabus daga mukaminsa na Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kano domin tsayawa takarar wannan kujera ta shugabanci.

 

 

 

 

Sauran manyan mukaman da aka zaba sun hada da:
Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo – Mataimakin Shugaba
Prof. Yusuf Muhammad Sabo Bichi – Sakataren Jiha
Hajiya Fatima Abdullahi Dala – Shugabar Mata

 

 

 

 

 

Sabon kwamitin zartarwa mai mambobi 28 ana sa ran zai kara hada kan jam’iyya tare da shiryawa  domin fuskantar kalubalen siyasa a nan gaba a jihar.

 

 

 

 

ga Jerin Sabbin Shugabanni:
Shugaba:
Hon. Umar Haruna Doguwa
Mataimakin Shugaba:
Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo
Sakataren Jiha:
Prof. Yusuf Muhammad Sabo Bichi
Mai Ba da Shawarar Shari’a:
Abdul Adamu Fagge SAN
Mataimakin Mai Ba da Shawarar Shari’a:
Barr. Bashir Yusuf Tudun Wuzirci
Ma’aji:
Kabiru Sule Rogo
Mataimakin Ma’aji:
Umar Yusuf Umar
Sakataren Kudi:
Ma’aruf Abdullahi Garo
Mataimakin Sakataren Kudi:
Mustafa Muhammad Kalwa
Sakataren Tsare-tsare:
Dr. Kabiru Hussaini Zawaciki
Mataimakin Sakataren Tsare-tsare:
Barr. Abdussalam Umar
Sakataren Yada Labarai (PRO):
Auwalu Abdullahi Sani Mai Nagge
Mataimakin Sakataren Yada Labarai:
Sani Fata Sharada
Sakataren Jin Kai:
Bashir Mai Sango
Mataimakin Sakataren Jin Kai:
Garba Hussaini Kwami
Mai Duba Kudi (Auditor):
Abubakar Salisu Makoda
Mataimakin Mai Duba Kudi:
Nura Muhammad Ingili
Shugabar Mata:
Hajiya Fatima Abdullahi Dala
Mataimakiyar Shugabar Mata:
Hajiya Habiba Abdullahi Takai
Shugaban Matasa:
Salisu Yahaya Hotoro
Mataimakin Shugaban Matasa:
Mussadiq Wada Waziri
Shugaban Masu Bukata Ta Musamman
Nura Umar Malami
Ex Officio I:
Alhaji Auwalu Nagero
Ex Officio II:
Alhaji Rabiu Nagoggo
Ex Officio III:
Alhaji Wada A.A Rano
Mataimakan Ex Officio:
Alhaji Musa Bagwai
Rahama Kabir Fagge

 

 

 

 

 

Sabon shugabancin na zuwa ne a wani lokaci da ake sa ran jam’iyyar za ta kara tsaurara shiri domin zabubbuka da harkokin siyasa masu zuwa a Jihar Kano.

You might also like
Leave a comment