Hukumar tsaro ta civil defence ( NSCDC ) reshen Jihar Kano ta gargadi ‘yan kwangila da masu gine-gine da su guji lalata igiyoyin fibre-optic yayin aikin tono ƙasa da gini
Kwamandan rundunar a jihar Mohammed Hassan-Agalama, ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Ibrahim Idris-Abdullahi, ya fitar a jahar Kano ranar Talata.
Hassan-Agalama ya nuna damuwa kan yawaitar lalacewar igiyoyin fibre na ƙarƙashin ƙasa sakamakon sakaci ko kuskure yayin ayyukan tono ƙasa. Ya ce irin waɗannan abubuwa na haddasa tangarda ga sadarwa, intanet, harkokin banki da sauran muhimman ayyuka da al’umma da ‘yan kasuwa ke dogaro da su.
Ya buƙaci kamfanonin gine-gine da masu haɓaka kadarori su nemi sahalewar da ta dace da izinin “right-of-way” kafin fara aikin tono ƙasa. Haka kuma ya shawarce su da su riƙa tuntuɓar kamfanonin samar da sabis domin gano da taswira hanyoyin da igiyoyin fibre ke bi kafin a fara tono ƙasa.
Kwamandan ya jaddada cewa dole ne wakilan fasaha na kamfanonin sadarwa su kasance a wurin yayin manyan ayyukan tono ƙasa domin kauce wa asarar dukiya mai yawa.
Ya ƙara da cewa, an ayyana igiyoyin fibre da sauran kayan aikin sadarwa a matsayin Muhimman Kadarorin Ƙasa da dokoki ke karewa. Don haka duk wanda aka samu da laifin lalata su da gangan, sakaci ko zagon ƙasa za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu
kwamanda Hassan-Agalama ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ƙara sa ido da gudanar da sintiri a wuraren gine-gine domin tabbatar da bin doka.
Ya kuma roƙi jama’a da masu ruwa da tsaki su riƙa kai rahoton duk wani motsi na zargi ko aikin tono ƙasa ba tare da izini ba kusa da hanyoyin fibre zuwa ofishin Civil Defence mafi kusa.
A ƙarshe, ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da kare muhimman kayayyakin more rayuwa domin bunƙasa tattalin arziki, tsaron jama’a da ci gaban ƙasa.