Shugaban kasa bola Ahmad tunibu ya nada Taiwo. Oyedele a matsayin Ministan Ƙasa na Ma’aikatar Kuɗi, domin maye gurbin Doris Anite-Uzoka.

A cewar sanarwar da mai baiwa  shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, an aika sunan Oyedele zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa, ta hannun Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.

 

 

 

Kafin wannan nadin, Oyedele shi ne shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Manufofin Haraji da Tsarin Kuɗaɗe. Ya shafe shekaru 22 yana aiki a kamfanin PwC, inda ya kai matsayin Fiscal Policy Partner da Africa Tax Leader. Haka kuma farfesa ne a Babcock University, kuma malami mai ziyara a Lagos Business School.

 

 

 

 

A nata bangaren, Anite-Uzoka za ta koma Ma’aikatar Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa a matsayin Ministar Ƙasa  wanda shi ne karo na uku tana rike da mukami a wannan gwamnati.

 

 

 

 

Wannan nadin na iya ƙara ƙarfafa sauye-sauyen da gwamnati ke yi a fannin haraji da tattalin arziki, musamman ganin ƙwarewar Oyedele a harkar gyaran tsarin kuɗi. Amma nasarar sa za ta dogara ne da yadda zai iya aiki tare da Majalisa da sauran masu ruwa da tsaki domin kawo sauyi mai amfani ga talakawa.

You might also like
Leave a comment