Kungiyar Matasa Arewa Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya ta baiwa hukumomin tsaro makamai nazamani

Kungiyar Arewa Youth Assembly (AYA) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara karfafa tsarin tsaron Najeriya ta hanyar bai wa hukumomin tsaro makamai na zamani,

 

 

 

 

 

 

 

alburusai, drones, da na’urorin tattara bayanan sirri  domin dakile ta’addanci da sauran laifuka a kasar.

 

 

 

 

 

 

 

 

Kungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja, inda ta kuma nuna damuwa kan abin da ta kira mayar da matsalar tsaro abin siyasa, tana mai gargadin cewa hakan na iya lalata hadin kan kasa da kuma kokarin da ake yi na yakar ‘yan ta’adda.

 

 

 

 

 

 

 

 

Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin kungiyar, Mohammed Danlami, ya ce yawaitar amfani da matsalolin tsaro wajen siyasa, musamman a lokacin zabe, abu ne mai hatsari kuma ba zai haifar da alheri ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ya ce: “Muna rokon Shugaba Bola Tinubu da ya bai wa hukumomin tsaro karin makamai, drones, ingantaccen tallafin sufuri da kayan aiki, da kuma na’urorin bayanan sirri na kai tsaye. Su kammala aikin, su farauto duk wani dan fashi ko dan ta’adda da ke aiki a kowanne suna,” in ji Danlami.

 

 

 

 

 

 

 

Danlami ya kara da cewa:
“Abu ne mai matukar tayar da hankali yadda ake rage matsalar tsaro ta kasa zuwa abin tattaunawar siyasa. Mutuwar mutane da rushewar al’umma bai kamata a rika amfani da su domin cin moriyar zabe ba.”

 

 

 

 

 

Ya jaddada cewa duk da cewa jam’iyyun adawa suna da hakkin kundin tsarin mulki na sa ido kan gwamnati, ya kamata hakan ya kasance cikin gina kasa, ba tare da rushe kokarin hadin gwiwar dawo da zaman lafiya ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

Har ila yau, Danlami ya bayyana damuwa kan yadda ake samun karin matsalar rashin tsaro a lokacin zabe, yana mai kira ga hukumomi da su binciki musabbabin hakan.

 

 

 

 

 

 

 

Ya ce: “Wannan al’amari yana haifar da tambayoyi masu muhimmanci da bai kamata a yi watsi da su ba. Muna ganin akwai bukatar gudanar da cikakken bincike domin gano tushen wadannan matsalolin tsaro da ke maimaituwa.”

 

 

 

 

 

 

Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, kakakin AYA ya ce ya halatta jama’a su nuna damuwa kan rashin tsaro, amma ya gargadi mutane da kada su rika tayar da hankali ta hanyar yada labarai cikin tsanani ko yin amfani da bala’i domin siyasa.

 

 

 

 

 

 

 

 

Ya ce  “A cikin al’umma mai wayewa, bai kamata a rasa ko da rai daya ba ba tare da dalili ba, kuma jama’a na da hakkin neman kariya. Amma amfani da irin wadannan masifu domin siyasa na rage hadin kan kasa tare da karkatar da hankali daga mafita.”

 

 

 

 

 

 

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan ba a magance rashin tsaro ba, zai iya janyo babbar illa ga tattalin arziki da kuma tsaron abinci.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ta ce: “Ba za a yi zabe ba idan Najeriya ta rushe. Idan rashin tsaro ya ci gaba da kara muni, zai iya rusa ba gwamnati kadai ba, har ma da tubalin kasa baki daya.”

 

 

 

Duk da haka, kungiyar ta yaba wa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, tana mai cewa an samu ingantaccen hadin kai da aiki mai kyau a ‘yan watannin nan.

 

 

 

AYA ta  yabawa:
Mai ba Shugaban Kasa shawara kan tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu
Shugabannin sojoji
Chief of Defence Staff, Janar Olufemi Oluyede
Chief of Army Staff, Janar Waidi Shaibu

 

 

 

 

Kungiyar ta ce tun bayan hawansu, an kubutar da daruruwan mutane da aka sace ba tare da biyan kudin fansa ba, sannan an tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a sassa daban-daban na kasa.

 

 

 

 

Danlami ya ce: “Karfin gwiwar sojoji ya dawo. Yanzu ana basu tallafi cikin lokaci, lada a filin daga, da karin taimako. Zamanin barin sojoji su mutu ba tare da dauki ba ya kare.”

 

 

Kungiyar ta kuma bukaci kafafen yada labarai su rika yin rahotanni cikin gaskiya da kulawa, tare da kira ga ‘yan kasa da su kasance masu sa ido da bayar da hadin kai ga hukumomin tsaro.

 

 

 

A karshe, AYA ta ce magance rashin tsaro abu ne da ke bukatar hadin kan kasa baki daya, ba tare da bambancin siyasa, kabila ko addini ba, tana mai jaddada cewa hadin kan jama’a da bayar da bayanan sirri ga hukumomi na daga cikin muhimman hanyoyin kawo karshen ta’addanci a Najeriya.

You might also like
Leave a comment