Gwamnan jahar zamfara Dauda Lawal Ya Lashe Kyautar BON Ta Gwamnan Shekara Kan Ayyukan Gine-gine a Zamfara

Kungiyar Broadcasting Organisations of Nigeria (BON) ta ba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, lambar yabo ta Gwamnan Shekara Kan Ayyukan Gine-gine

 

 

 

 

 

 

Governor of the Year) bisa manyan ayyukan da gwamnatinsa ke yi a shirin sabunta birane a jihar.

 

 

 

 

 

 

 

Gwamnan ya karɓi wannan lambar yabo ne a yayin bikin Nigeria Broadcasting Awards karo na biyu da aka gudanar a Cibiyar Taron NAF da ke Abuja.

 

 

 

 

 

A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa BON ta yaba da gagarumar nasarar Zamfara wajen ayyukan more rayuwa, inda ta ce jihar ta samu sauyi mai girma da ba a taba ganin irinsa ba.

 

 

 

 

 

 

 

Sanarwar ta ce BON ta amince da irin nasarorin da aka samu a Zamfara, wanda ya zarce ma fannin yada labarai, domin nuna kwarewa da nagarta.

 

 

 

 

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Sulaiman Bala Idris, tare da John Momoh, Shyngle Wigwe, Abubakar Jijiwa, da Sa’a Ibrahim, na daga cikin fitattun ’yan Najeriya da aka karrama a BON Awards 2026.

 

 

 

 

 

 

 

A wani bangare na sanarwar an ce:
“BON wata kungiya ce da ke hada gidajen rediyo da talabijin na gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya, wadda aka kafa a shekarar 1973 domin kare muradun harkar watsa labarai da tabbatar da ingantattun ka’idojin aikin jarida.”

 

 

 

 

 

 

 

Sanarwar ta ce kungiyar ta gudanar da dogon bincike na tsawon watanni domin zaben wadanda suka cancanta, da nufin karfafa nagarta da inganta ka’idojin aikin watsa labarai a Najeriya.

 

 

 

 

 

 

 

 

Kwamitin zaben lambar yabon ya kasance karkashin jagorancin Dr. Danladi Bako, tsohon Darakta Janar na Hukumar NBC, tare da mambobi daga ARCON da NBC.

 

 

 

 

 

 

Kwamitin ya bayyana cewa sun ba Gwamna Dauda Lawal wannan lambar yabo ne saboda gagarumin ci gaban da ya samu a fannoni da dama, musamman wajen sauya Gusau zuwa babban birni na zamani.

 

 

 

 

 

 

 

 

Sanarwar ta ce Zamfara ta samu manyan nasarori a karkashin Gwamna Lawal, ciki har da fara gina tashar jirgin sama ta kasa da kasa (International Airport) a jihar.

 

 

 

 

 

 

 

Baya ga ayyukan sabunta birane da kuma gina da gyara asibitocin gwamnati, gwamnatinsa ta gina, ta gyara, tare da samar da kayan aiki ga makarantu sama da 800 a dukkan kananan hukumomi 14 na jihar.

 

 

 

 

 

 

 

A karshe, sanarwar ta ce wannan karramawa daga babbar hukumar watsa labarai a Najeriya zai kara wa gwamnan kwarin gwiwa wajen ci gaba da kokarinsa na yi wa al’ummar Zamfara hidima da kuma sake gina jihar.

You might also like
Leave a comment