Ana Zargin yan Boko Haram da Kashe Kwamandan Birgede awani Sabon Hari a borno

Rahotanni sun nuna cewa Kwamandan Birged na rundunar Joint Task Force da ke Benisheikh a Karamar Hukumar Kaga ta Jihar Borno, Brig. Gen. O. O. Braimah, ya rasa ransa sakamakon wani sabon hari da ake zargin ’yan Boko Haram/ISWAP suka kai da tsakar dare.

 

 

 

 

 

 

 

Majiyoyin cikin gari sun ce an kashe fararen hula, wani ɗan Civilian JTF, jami’an tsaro, da kuma ’yan Boko Haram/ISWAP da dama, lokacin da ’yan ta’addan suka kai hare-hare a lokaci guda a garin Benisheikh da kuma al’ummar Pulka da ke Karamar Hukumar Gwoza.

 

 

 

 

 

 

Sun ce ’yan ta’addan sun kai hari garin Benisheikh da misalin karfe 1:00 na dare a safiyar Alhamis, inda suka kona manyan motoci   tare da lalata motoci na kasuwanci.

 

 

 

 

 

Motoci da fasinjoji da dama da ke kan hanya sun makale a garin saboda rufe hanyar Maiduguri–Damaturu da ake yi kullum da yamma, lamarin da ya tilasta musu kwana a Benisheikh.

 

 

 

 

 

 

 

 

A cewar majiyoyin, Brig. Gen. Braimah ya rasa ransa yayin gumurzu mai tsanani.
Wani daga cikin mazauna garin ya ce:

 

 

 

 

 

 

“An kashe ’yan ta’adda da dama a Benisheikh, amma abin takaici wasu jami’an tsaro ciki har da kwamandan birged sun sadaukar da rayukansu, sannan ’yan ta’addan sun tafi da wasu motoci.”

 

 

 

 

 

 

 

A wani sakon da ya wallafa a Facebook, wani mazaunin Benisheikh mai suna Malam Lawal Benisheikh ya ce:

“Innalillahi wa Inna’illaihin raji’un. Boko Haram sun sake yin nasarar kashe kwamandan rundunar Benisheikh. Wannan mummunan abu ya faru jiya da dare lokacin da suka kai hari sansanin sojoji da yawa. Allah ya jikansu.”

 

 

 

 

Wasu majiyoyi sun ce ’yan ta’addan sun fara kai hari ne a Pulka da Bakin Ruwa, duk a Karamar Hukumar Gwoza, da misalin karfe 10:30 na dare ranar Laraba, inda suka mamaye wani sansanin sojoji suka kona kayan yaki da dama.

 

 

 

 

 

Daga bisani, da misalin karfe 1:00 na dare, sun kai wani sabon hari a Benisheikh da Ngamdu, inda suka mamaye 29 Task Force Brigade, suka lalata motocin sojoji da dama.
Rahotanni sun kuma ce ’yan ta’addan sun kwashe kayan abinci daga shaguna a Pulka, tare da lalata wasu abubuwa da suka hada da injuna da kayan aikin wani kamfanin gina hanya.

 

 

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Pulka na dauke da dubban ’yan gudun hijira daga garin Ngoshe, wadanda suka tsere bayan Boko Haram sun kai musu hari kimanin wata guda da ya wuce.

 

 

 

 

 

 

Har zuwa yanzu, Hedkwatar Joint Task Force  Operation HADIN KAI ba ta fitar da sanarwa a hukumance game da hare-haren ba.

You might also like
Leave a comment