Shugaba Tinubu Ya Bayyana shirin gwamnatinsa na inganta aikin yansada masu tantara bayanan sirri

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin kara zuba jari a bangaren horar da ’yan sanda, tattara bayanan sirri  da kuma amfani da sabbin na’urorin zamani domin inganta aikin rundunar ’yan sandan Najeriya  zuwa matakin rundunar da za ta iya yin gogayya da ta kasashen duniya.

 

 

 

 

 

 

Ya ce Najeriya na da nauyin ɗabi’a na dindindin na tallafa wa jami’an tsaro, domin zaman lafiyar kasa yana dogara ne da irin kariya da jajircewar jami’an da ke tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

 

 

 

 

 

Wannan na cikin wata sanarwa da Stanley Nkwocha, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, ya fitar a yau.

 

 

 

 

 

 

Sharudan da Tinubu ya nuna za a mayar da hankali a kansu ga jami’an ’yan sanda sun haɗa da:
Karin horo na zamani domin kwarewa wajen aiki da tsaro.

 

 

Inganta tattara bayanan sirri domin gano barazana tun kafin ta faru.

Samar da kayan aiki na zamani kamar na’urorin bincike, sadarwa, da fasahar zamani.

 

Karfafa tsarin aiki na ƙwararru domin rundunar ta zama mai nagarta da inganci.

Kula da walwala da jin dadin jami’an ’yan sanda, domin su yi aiki cikin kwanciyar hankali.

Karfafa ɗabi’a da gaskiya a aikin ’yan sanda domin yaki da cin hanci da rashawa.

Daga martabar rundunar NPF ta zama runduna ta zamani mai bin doka da kare hakkin jama’a.

 

 

 

 

 

 

Tinubu ya jaddada cewa idan har ana son Najeriya ta samu cikakken zaman lafiya, dole ne gwamnati ta ci gaba da karfafa jami’an tsaro ta hanyar horaswa, kayan aiki, da kyakkyawan tsarin aiki.

You might also like
Leave a comment