’yan bindiga sun kashe mutum 3, tare da jikkata wasu dadama a Nijar

’Yan bindiga sun kai hari kauyukan Lanta, Tunga da Bagna da ke Erena Ward a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Niger, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama.

 

 

 

 

 

Rahotanni sun nuna cewa harin ya fara ne da misalin karfe 10:30 na safe a ranar Talata a Bagna, wanda shi ne garin tsohon Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Niger, Emmanuel Umar, kafin daga bisani ya bazu zuwa kauyukan makwabta.

 

 

 

 

 

 

Wata majiya daga Bagna ta shaida wa Daily Trust cewa, duk da ana zargin adadin wadanda abin ya shafa ya fi haka yawa, har yanzu ba a tabbatar da hakikanin yawan ba saboda har yanzu ana cikin fargaba da tashin hankali.

 

 

 

 

 

Majiyar ta ce maharan sun shigo ne da yawa a kan babura, kuma sun yi ta kai farmaki na tsawon lokaci ba tare da wani ya hana su ba.
“Zuwa yanzu mun gano gawarwaki uku. Wasu da dama sun samu raunuka daban-daban. Mutane da yawa sun tsere zuwa garin Erena, wanda shi ne kadai wurin da ake ganin yana da dan aminci a kusa. Muna kira ga gwamnati da ta kawo mana dauki,” in ji majiyar.

 

 

 

 

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Niger, Barrista Maurice Bello Magaji, ya tabbatar da faruwar lamarin ta cikin sakon tes da ya tura wa wakilinmu.

 

 

 

Ya ce: “Eh, gwamnati ta samu sahihin bayani kuma tana aiki tare da jami’an tsaro.”

You might also like
Leave a comment