Yan Sanda, Sojoji da ’Yan Bijilanti Sun Dakile Harin ’Yan Bindiga a Katsina, Jami’i 1 Yarasa ransa.
Rundunar haɗin gwiwa ta ’Yan Sanda, Sojoji, Katsina State Community Watch Corps da kuma ’yan sa-kai (vigilantes) ta samu nasarar dakile harin ’yan bindiga a Karamar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar, DSP Abubakar Sadik Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Ya ce a ranar 5 ga Afrilu, 2026, wasu da ake zargin ’yan bindiga ne dauke da muggan makamai sun fito da yawa, suka tare hanyar Karadua–Musawa a Matazu, inda suka bude wuta kan wata motar Volkswagen Golf, suka kashe mutane biyu nan take.
²Bayan samun rahoton lamarin, rundunar haɗin gwiwa ta gaggauta zuwa wurin, ta kore maharan, sannan ta kwashe wadanda abin ya shafa zuwa wani asibiti kusa.
Sanarwar ta kara da cewa ’yan bindigar sun sake taruwa, suka yi yunƙurin kai hari ofishin ’yan sanda na Matazu Division, amma jami’an tsaron da ke bakin aiki sun mayar da martani, suka dakile harin tare da dawo da zaman lafiya.
Sai dai an bayyana cewa, jami’in ɗan sanda guda ɗaya ya rasa ransa yayin musayar wuta.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Ali Umar Fage, ya tura karin jami’ai da kayan aiki domin ƙarfafa tsaro da hana sake kai hare-hare. Haka kuma, an fara bincike domin kamo wadanda suka aikata laifin.
Kwamishinan ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu da kuma na jami’in da ya rasu, sannan ya bukaci jama’a su kwantar da hankali su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro hadin kai, domin tabbatar da an kamo masu laifin.
Ya ce za a ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani nan gaba.