Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace uwa da ‘ya’ya 4 a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari a jihar Kaduna inda suka sace mambobin wani gida a Kurmin-Uwa, kusa da Janjala a Karamar Hukumar Kagarko.

 

 

 

 

 

 

 

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:23 na dare a ranar Juma’a, kamar yadda wani mazaunin Kagarko, Ibrahim Shehu, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho.

 

 

 

 

 

 

Ya ce da ‘yan bindigar suka shiga ƙauyen, sai suka nufi wani gida kai tsaye wanda suke nema, sannan suka kwashe mutane daga ciki.
Wadanda aka sace sun hada da uwa da ‘ya’yanta, kuma an bayyana sunayensu da suka hada da:
Ladi Malachy
Patience Malachy
Promise Malachy
Inama Malachy
Peter Malachy
Aboyi Malachy

 

 

 

 

 

Wani shugaban al’umma da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ya sanar da jami’an tsaro bayan samun kiran gaggawa cewa ‘yan bindiga sun mamaye ƙauyen Kurmin-Uwa, wanda yake kimanin kilomita 2 daga garin Kagarko.

 

 

 

 

 

 

“Da na samu kiran cewa ‘yan bindiga sun shiga Kurmin-Uwa, nan take na sanar da jami’an tsaro, amma ban san ko sun amsa ba,” in ji shi.

 

 

 

 

 

Ya ce har yanzu ba a samu tuntubar masu garkuwa da mutanen ba, kuma ya nuna damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ta ƙaruwa a ƙauyukan Kagarko.

 

 

 

 

 

Wani jami’in tsaro ya ce shi ma yanzu yake jin labarin, domin suna cikin daji tun ranar Talata suna kokarin gano maboyar ‘yan bindiga a yankin Kachia, domin ceto mutanen da aka sace a Katari ranar Laraba.

 

 

 

 

 

 

 

A halin yanzu, kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Hassan Mansur, bai amsa kiran waya ba, kuma bai mayar da martani ga saƙon da aka tura masa ba.

You might also like
Leave a comment