Mutane 11 sun mutu, an kone. gidaje 52 yayin wani rikici daya barke a Nasarawa

Aƙalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu, yayin da sama da gidaje 50 suka kone a wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a ƙauyukan Akyawa da Udege Kasa da ke Karamar Hukumar Nasarawa, a ranar Juma’a.

 

 

 

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Lafia.

 

 

 

 

 

 

Ya ce wasu da ake zargi ‘yan daba ne sun kai harin ramuwar gayya ne sakamakon zargin kashe wasu mutane biyu daga cikinsu.
“A yayin harin, mutane 11 sun mutu, sannan kimanin gidaje 52 sun kone a cikin ƙauyukan biyu,” in ji Nansel.

 

 

 

 

 

Nansel ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Shetima Mohammed, ya jagoranci tawaga zuwa wuraren da abin ya shafa domin duba irin barnar da aka yi da kuma tabbatar da dawo da zaman lafiya.

 

 

 

 

Ya ce CP ɗin ya nuna matuƙar alhini kan wannan mummunan lamari, tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da al’ummomin da abin ya shafa, yana mai tabbatar musu da cewa rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar da an yi adalci.

 

 

 

 

 

A cewar Nansel, CP ya bayar da umarnin a fara farautar masu aikata laifin, tare da tura ƙungiyoyin dabaru da jami’an bincike domin gano su, kama su, da gurfanar da su gaban kotu.

 

 

 

 

 

Domin hana sake ɓarkewar rikici, CP ya kuma bayar da umarnin ƙarfafa tsaro da ci gaba da tura jami’an ‘yan sanda zuwa yankin.

 

 

 

Ya kuma ce ‘yan sanda na aiki tare da sojoji da kuma NSCDC domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

 

 

 

Har ila yau, an gudanar da taron masu ruwa da tsaki yayin ziyarar, inda CP ya shawarci jama’a da su kwantar da hankali, su kasance masu bin doka, tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin taimakawa bincike.

 

 

 

 

 

 

Nansel ya tabbatar da cewa an riga an dawo da zaman lafiya a yankunan, kuma an ɗauki matakan kariya domin hana sake faruwar tashin hankali.

You might also like
Leave a comment