Babar kotun shariar musulinci dake filin hockey ta dage sauraron shari,ar da iyalan marigayi Alhji babale ila suka shigar da wasu mutane biyu akan rabon godo
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake zaman ta a Filin Hockey Karkashin jagorancin mai shari’ah Dr. Umar Sunusi Dan Baba, ta Cigaba da sauraron shari’ar Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila da suke Neman a raba musu Gadon wani Gareji.
A zaman kotun na wannan rana, masu kara, Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila sun hallara a gaban kotun tare da lauyan su Abbas Sulaiman Magashi.
Yayin da a bangaren wadanda ake kara na 1 Dana 2 basu bayyana a gaban kotun ba kuma lauyoyin su basu zo ba.
Inda kotun ta bayar da Umarnin aikewa da sammaci ga wadanda ake kara na 1 Nasiru Baballe Ila da Wanda ake kara na 2 Alhaji Yusuf Garba Ali.
Tunda farko dai, Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila ne suka shigar da rokon a raba musu Gadon wani Gareji da Mahaifin su ya rasu ya bari, sai kuma kwatsam wani Mutum me suna Alhaji Yusuf Garba Ali ya bayyana cewar wannan Garejin Mallakin sa ne sakamakon siyan da yayi a wajen Nasiru Baballe Ila.
Jin hakan ne tasa Iyalan marigayi Alhaji Baballe Ila suka Garzaya Babbar kotun shari’ar Musulunci dake zaman ta a Filin Hockey suka shigar da kara domin tabbatar da an fitar wa da kowanne bangare hakkin sa.
Yanzu haka dai, Sama da Shekaru 2 kenan ana Cigaba da sauraron wannan shari’ah duk da kasancewa an daukaka kara zuwa Babbar kotun Daukaka kara ta Addinin Musulunci, Wanda itama tayi Hukunci akan a dawo kotun kasa domin ta sake sauraron karar ta kuma raba musu Gadon wannan Garejin.