Gwamnan kaduna Uba Sani Ya Nemi Haɗin Gwiwa Da hukumar Tsara Birane domin tsara gine gine a jahar

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tukuru domin tabbatar da  gaskiya a rabon filaye,

 

 

 

da kuma ƙarfafa dokokin kula da gine-gine, da kuma inganta bunƙasar birane cikin tsari.

 

 

 

 

 

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar na zuba hannun jari a harkokin ababen more rayuwa da kuma shirin sabunta birane, domin inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna.

 

 

 

 

 

An bayyana hakan ne ta bakin Mataimakiyar Gwamna, Dakta Hadiza Balarabe, wadda ta wakilci gwamnan yayin da Cibiyar Masu Tsara Birane ta Najeriya (NITP) ta kai masa ziyarar girmamawa a Sir Kashim Ibrahim House.

 

 

 

 

 

 

Gwamnan ya ce gwamnati na ci gaba da yin gyare-gyare domin ƙarfafa tsare tsare  birane da gudanar da harkar filaye.

 

 

 

 

 

Sai dai ya jaddada cewa gwamnati ba za ta iya yin hakan ita kaɗai ba.

 

 

 

 

 

← Back

Thank you for your response. ✨

“Mun san gwamnati ba za ta iya yin wannan aiki ita kaɗai ba. Muna buƙatar ilimi, shawarwari, da haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙwararru irin naku. Rawar da kuke takawa wajen tabbatar da bin ƙa’idoji, gina ƙwarewa, da ƙarfafa sabbin dabaru a aikin tsara birane na da matuƙar muhimmanci wajen cimma ci gaban da ya dace,” in ji shi.

 

 

 

 

 

Gwamnan ya ce gwamnatinsa na da cikakken shiri na ci gaban karkara da birane, inda ya bayyana cewa:

 

 

 

 

 

 

“Babban shirin ci gaba mai ɗauke da gagarumin aikin gine-ginen ababen more rayuwa ya zama abin da muka fi bai wa muhimmanci.”

 

 

 

 

 

 

Ya kuma roƙi mambobin cibiyar NITP da su ci gaba da bayar da shawarwari da fasaha, musamman kan yadda amfani da fili ke shafar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

 

 

 

 

Gwamna Uba Sani ya kuma tuna da tsohon tarihin haɗin gwiwa tsakanin Jihar Kaduna da NITP.

 

 

 

“Jihar mu ta kasance da tsarin ci gaban tun shekarar 1913, inda aka samar da Master Plans, Spatial Development Framework, da kuma tsarin ababen more rayuwa. Wannan tarihi na nuna irin jajircewar NITP wajen tabbatar da ci gaban jiharmu cikin tsari,” in ji shi.

 

 

 

 

 

Gwamnan ya bayyana cewa Jihar Kaduna na daga cikin jihohin farko da Bankin Duniya (World Bank Group) ya zaɓa domin aiwatar da shirin mallakar fili, rijista, da takardun filaye a Najeriya.

 

 

 

 

 

 

 

Ya ce a makon da ya gabata, wata tawaga daga Bankin Duniya da Ma’aikatar Gidaje da Ci gaban Birane ta Tarayya sun ziyarci jihar domin duba yadda ake tafiyar da harkar filaye da tsarin mulki.

 

 

 

 

 

 

A ƙarshe, gwamnan ya ce ziyarar tawagar NITP ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban NITP, Farfesa Kingsley Ogboli, tare da mambobin Town Planners Registration Council of Nigeria, na ba da dama domin haɗa kai da tsara hanyoyin haɗin gwiwa.

 

 

 

 

 

inda  yace  Jihar Kaduna a shirye take kuma ta kuduri aniyar yin aiki tare da ku domin gina birane da al’umma masu tsari, haɗin kai, tsaro, da cigaban tattalin arziki,” in ji shi.

You might also like
Leave a comment