Kotu Ta Dage Sauraron Neman Belin malam Nasiru El,Rufa,i Zuwa 14 ga Afrilu
Wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta dage sauraron bukatar beli da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya shigar zuwa ranar 14 ga Afrilu.
Alkalin kotun, Mai shari’a Rilwanu Aikawa, ya sanya ranar ne bayan ya saurari hujjojin bangaren kariya da kuma na masu gabatar da kara a ranar Laraba.
An gurfanar da El-Rufai ne gaban kotu ta hannun Hukumar ICPC, bisa tuhuma 10 da suka shafi zargin maida kadarorin gwamnati mallakarsa da kuma wanke kudaden haram
El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, inda ya ce bai aikata laifin ba.
Kotun ta umarci cewa El-Rufai ya ci gaba da zama a tsare a hannun ICPC, har zuwa ranar da za a saurari bukatar belin.
Bayan zaman kotun, wani daga cikin lauyoyinsa, Ubong Akpan (SAN), ya tabbatar da dage sauraron belin, amma ya ce shugaban tawagar lauyoyin zai yi karin bayani ga manema labarai daga baya.