Yan Bindiga Sun Sace wasu masu Hada Gawayi su Takwas a Plateau

Wasu ’yan bindiga sun sace masu hura gawayi takwas a yankin Nyalun, da ke Bashar District a Karamar Hukumar Wase ta Jihar Plateau.

 

 

 

 

 

 

Lamarin ya faru ne da yammacin Talata, yayin da mutanen ke dawowa gida bayan sun gama sarrafa gawayi a wajen gari.

 

 

 

 

 

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, wani jagoran matasa a Wase mai suna Shapi’i Sambo ya ce tun farko maharan sun sace mutane 10 da ke cikin motar, amma daga baya sun saki biyu a Garga da ke Karamar Hukumar Kanam, domin su kai sakon neman kudin fansa.

 

 

 

 

 

 

“Mutanen suna dawowa kusan 7:30 na yamma ne sai maharan suka tare motarsu wadda take dauke da gawayi suka tafi da su,” in ji Sambo. “Abin takaici ne matuka, domin mutanen nan suna kokarin neman halal ne don su rayu.”

 

 

 

 

 

 

An bayyana sunayen wadanda aka sace da suka hada da:
Hassan Sa’idu
Shamsudden Abubakar
Usamatu Yakubu
Dayyabu Usman Waziri
Inkilulu Dauda
Ado Sambo
Sule Dahiru
Umar Amadu

 

 

 

 

 

 

Sambo ya kara da cewa ana zargin maharan sun tafi da su zuwa dajin Kukawa, wanda ake cewa yana zama maboyar ’yan ta’adda a yankin.

 

 

 

 

 

Daya daga cikin wadanda aka saki, Mummuni Musa, ya ce an daure shi da wani mutum kafin daga bisani a sake su domin kai sakon fansa.

 

 

 

 

 

“Sun ce mu koma gida mu gaya wa mai motar ya sayar da motar domin a biya kudin fansar mutanen takwas,” in ji shi.

 

 

 

 

 

 

A ‘yan shekarun nan, yankunan Wase da Kanam sun fuskanci yawaitar sace-sace da ta’addanci.

 

 

 

 

Wannan lamari ya biyo bayan wani rahoto da ya bayyana cewa kusan makonni biyu da suka wuce, wasu ’yan bindiga sun kashe sojoji da ’yan sa-kai a Karamar Hukumar Kanam.

 

 

 

 

 

An ce kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda ta Plateau, DSP Alabo Alfred, bai yi nasara ba har zuwa lokacin.

You might also like
Leave a comment