Tinubu Yayi Ganawar sirri da Ganduje da Badaru a Aso Rock

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da kuma tsohon Ministan Tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar, a wasu ganawa daban-daban a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Aso Rock, Abuja, a ranar Talata.

 

 

 

 

 

 

An gudanar da ganawar ne a sirrance  inda babu ɗayansu da ya bayyana dalilin da ya kai su ganawa da shugaban ƙasa.

 

 

 

 

 

‘Yan jarida sun lura cewa Ganduje, sanye da babbar riga, ya bar fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4:15 na yamma, yayin da Badaru ya fita kusan mintuna 15 bayan haka da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

 

 

 

 

 

Wannan ya nuna cewa ganawar ba tare aka haɗa su ba, sai dai kowa ya gana da shugaban ƙasa a nasa lokaci.

 

 

 

 

 

 

Ganduje ya riƙe muƙamin Shugaban APC na ƙasa daga watan Agusta 2023 zuwa Yuli 2025, kafin ya sauka daga muƙamin. Daga bisani, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya gaje shi, bayan an zaɓe shi a matsayin cikakken shugaban jam’iyyar a Babban Taron Zaɓen Shugabannin Jam’iyyar APC karo na 4 da aka gudanar ranar 27 ga Maris, 2026, a Eagle Square, Abuja.

 

 

 

 

 

Kafin zama shugaban jam’iyya, Ganduje ya kasance Gwamnan Jihar Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023.

 

 

 

 

 

Shi kuwa Badaru, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa ne daga 2015 zuwa 2023, kuma kwanan nan ya yi murabus daga muƙamin Ministan Tsaro a gwamnatin Tinubu.

You might also like
Leave a comment