Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin magance matsalar tsaro da ya addabi arewanci Nigeria da kuma bada Umarnin Bincike, kan hari da ya shafi fararen hula da kuma Tallafa wa Waɗanda Abin Ya Shafa
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tana nan daram kan ƙudirinta na kawar da ta’addanci da ‘yan bindiga a ƙasar nan,
tare da jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da irin waɗannan mummunan al’amura domin raunana ƙudurin ƙasa ko kuma rushe ƙoƙarin Sojojin Najeriya ba.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa inda ya ce gwamnati na aiki tare da gwamnatocin jihohin Borno da Yobe, da kuma hukumar NEMA da SEMA, domin bayar da agajin jin ƙai ga iyalan da abin ya shafa sakamakon sabbin hare-haren soji da aka kai wa ‘yan ta’adda a jihohin da abin ya shafa.
ministan Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan lamarin, domin duba bayanan sirri, tsarin zaɓon hari, da yadda aka aiwatar da shi, domin gano duk wata giɓi da kuma tabbatar da ɗaukar mataki idan akwai laifi.
Ministan ya ce kare rayukan fararen hula na daga cikin manyan aiyukan Sojojin Najeriya, kuma suka jajirce wajen ƙara inganta daidaito, ɗaukar alhaki, da ci gaba da ɗaukar matakai har sai an samu zaman lafiya mai ɗorewa.
Ya kuma bayyana cewa harin da aka kai kan wuraren ‘yan ta’adda da aka tabbatar a yankin Jilli da ke ƙaramar hukumar Gubio a jihar Borno, a ranar 11 ga Afrilu 2026, wanda Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai ƙarƙashin Operation HADIN KAI, aiki ne na gangan bisa sahihan bayanan sirri, ba wai hari ne na bazata ba ko na rashin bambanci ba.
Sanarwar ta ce an kai harin ne bayan dogon lokaci ana tattara bayanan sirri, sa ido da bincike, inda aka tabbatar cewa yankin Jilli na aiki a matsayin kasuwar ‘yan ta’adda.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce an rufe kasuwar a hukumance shekaru biyar da suka wuce saboda ‘yan ta’adda sun mamaye yankin, kuma ya bayyana yankin a matsayin cibiyar ayyukan ta’addanci.
Gwamnatin Tarayya ta bukaci fararen hula su riƙa bin shawarwarin tsaro, su guji shiga wuraren da aka haramta, kuma su ba jami’an tsaro haɗin kai.
Haka kuma, gwamnatin ta bukaci kafafen yaɗa labarai su kasance masu ɗaukar nauyin gaskiya wajen rahoton al’amuran tsaro, tana mai cewa rahoton da ba a tabbatar da sahihancinsa ba.
Ministan ya bayyana cewa daga cikin nasarorin gwamnati ke samu a yaƙin da ta’addanci akwai samun hukunci kan wasu ‘yan Boko Haram da ISWAP, inda aka yanke musu hukunci har da ɗaurin rai da rai, ciki har da waɗanda aka samu da laifin bayar da tallafi ko taimakon kayan aiki ga ‘yan ta’adda.
A ƙarshe, Gwamnatin Tarayya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda abin ya shafa tare da nuna juyayi ga waɗanda suka samu raunuka