Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta Gayyaci Waɗanda sunayesu suka fita na neman aiki da NAF da su Halarci Tattaunawar BMTC 46
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta gayyaci ‘wadanda aka fitar da sunayensu na neman ɗaukar ma’aikata da ta gudanar, domin halartar tattaunawar Kwamitin tantancewa ta BMTC 46/2025 wadda za a gudanar a jihar Kaduna.
Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 15 ga Afrilu 2026, inda ya ce za a gudanar da wannan shirin a NAF Base, Kaduna, daga ranar 27 ga Afrilu zuwa 13 ga Yuni 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da suka cancanta kawai su ne waɗanda suka yi nasara a Jarabawar Zonal General Aptitude Test da aka gudanar ranar 5 ga Disamba 2025, a sansanonin NAF guda 15,
kuma sunayensu suka bayyana a shafin ɗaukar ma’aikata na hukuma.
An ce ana iya duba sunayen a shafin yanar gizo na NAF: nafrecruitment.airforce.mil.ng/updates/
Rundunar ta umarci duk waɗanda aka fitar da sunayensu su bi dukkan umarnin da aka bayar a shafin domin shiryawa yadda ya kamata.
NAF ta jaddada cewa dukkan tsarin ɗaukar ma’aikatan kyauta ne, kuma ba a yarda wani ya biya kuɗi a kowane mataki ba.
Sanarwar ta yi gargaɗi ga jama’a da su guji ‘yan damfara, tana mai cewa: “Dukkan tsarin ɗaukar ma’aikata kyauta ne. Kada wani ya biya kuɗi a kowane mataki.”