Kutu ta yake hukuncin daurin shekaru 15 ga wani da ake zargi da safarar kwaya a Kano
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen jahar Kano ta ce katu ta yake hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari kan wani matashi dan shekara 20 mai suna Muhammad Maharazu, bisa laifukan mallakar miyagun kwayoyi da kuma yunkurin kai wa jami’an hukuma hari.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Alhamis a Kano.
Ya ce an yanke hukuncin ne a ranar 15 ga Afrilu, 2026, ta hannun Mai Shari’a S.M. Shuaibu na Kotun Tarayya dake zamanta a Kano.
Muhammad-Maigatari ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin a ranar 14 ga Fabrairu, 2026, a wani sanannen a wajen sayar da miyagun kwayoyi na Filin Idi, inda jami’an rundunar musamman ta hadin gwiwa (Commander’s Special Joint Task Force) suka kama shi.
Ya ce an same shi da wasu nau’ikan haramtattun kwayoyi, ciki har da allunan Diazepam.
“Yayin da jami’an ke binsa, sai ya fito da wata doguwar wuka domin ya kai musu hari don ya tsere.
“Amma an kwace wukar cikin dabara, aka kama shi sannan aka gurfanar da shi a kotu,” in ji shi.
A cewarsa, kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari ba tare da zabin tara ba, kuma hukuncin zai fara aiki ne daga ranar da aka yanke hukuncin.
Kwamandan NDLEA a Kano, Malam Dahiru Yahaya-Lawal, ya yabawa kotu bisa wannan hukunci, yana mai cewa hukuncin ya nuna tsauri da adalci.
“Wannan hukunci ya nuna karara cewa babu wata barazana ko tashin hankali da zai hana jami’anmu gudanar da aikinsu.
“Kano ba za ta zama mafakar masu fataucin kwayoyi ba. Ko kadan ne aka kama da shi, za a gurfanar da ni agaban kotu i,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa wannan hukunci zai zama darasi ga sauran mutane, musamman wadanda ke amfani da tashin hankali wajen kin amincewa da kama su.
Ya bukaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumar hadin kai domin kawar da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.
Yahaya-Lawal ya jaddada cewa yaki da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi nauyi ne na kowa da kowa. (NAN)