Jam’iyyar Labour Party ta ayyana ranar 23 ga Mayu, 2026 domin gudanar da zaben fidda gwani na shugaban ƙasa don tunkarar banban zaben 2027

Mai ba shugaban rikon kwarya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ken Asogwa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

 

 

 

 

 

Ya ce wannan na daga cikin jadawalin da kwamitin zartarwa na kasa (NEC) ya amince da shi, a wani taro da Independent National Electoral Commission (INEC) ta halarta.

 

 

 

 

 

Muhimman ranaku a jadawalin:
15 ga Afrilu, 2026 – Mika kundin rajistar mambobi ga INEC
11 ga Afrilu, 2026 – Taron ƙasa (National Convention)
15 ga Mayu, 2026 – Fitar da ‘yan takara na gwamnoni da majalisu
23 ga Mayu, 2026 – Zaben fidda gwani na shugaban ƙasa

 

 

 

 

 

Hakazalika, an tsara gudanar da zaɓen ƙananan matakai kamar haka:
26 ga Maris – Matakin mazabu (Ward Congresses)
28 ga Maris – Matakin ƙananan hukumomi
31 ga Maris – Matakin jihohi

 

 

 

 

 

 

Sauran muhimman batutuwa:
NEC ta amince da ƙaddamar da rajistar mambobi ta zamani (e-registration) tare da na hannu domin ƙarfafa tsarin jam’iyya.

 

 

 

 

 

An kuma ba shugabannin jam’iyyar ikon naɗa rikon kwarya a guraben da babu shugabanni domin ci gaba da tafiyar da aiki.

 

 

 

 

 

 

Kwamitin amintattu (BOT) ya dakatar da wasu mambobi bisa zargin rashin ɗa’a da ayyukan da suka sabawa jam’iyya.
Bugu da ƙari, NEC ta marawa shugabancin Nenadi Usman baya a matsayin shugabar rikon kwarya, bayan hukuncin kotu da ya tabbatar da ita.

 

 

 

 

 

Jam’iyyar ta kuma yaba wa Independent National Electoral Commission (INEC) bisa bin umarnin kotu cikin gaggawa.

You might also like
Leave a comment