Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da tsare tsaren yadda za,a gudanar da gudanar da bikin Eid al-Fitr (Sallah)
Gwamnati ta ce ta samu sahihan bayanan tsaro da ke nuna cewa wasu mutane na shirin haddasa rikici a lokacin bikin Sallah, don haka dole ne a ɗauki matakan kariya domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi.
Tsarin yadda za a gudanar da Hawan Sallah
Hawan Idi:
Za a gudanar da shi karkashin jagorancin Muhammadu Sanusi II daga filin sallar Idi na Kofar Mata, ya bi hanyoyin da aka tsara har zuwa fadar sarki a Kofar Fatalwa.
Hawan Nasarawa:
Za a yi shi amma ba dawakai ba (wato an rage wasu abubuwa na al’ada domin tsaro).
Hawan Daushe:
An dakatar da shi na wucin gadi, za a mayar da shi zuwa wasu lokutan Sallah na gaba.
Hawan Fanisau da Dorayi:
Su ma an dakatar da su a halin yanzu domin kauce wa matsalolin tsaro.
Umarnin tsaro
An umarci jami’an tsaro da su:
Ƙara tsaurara sintiri da sa ido
Tabbatar da bin dokoki da umarnin gwamnati
Daukar matakan doka kan duk wanda ya karya zaman lafiya
Gwamnati ta roƙi al’umma da su:
Zauna lafiya da bin doka
Guji yaɗa jita-jita ko labaran ƙarya
Ba jami’an tsaro haɗin kai
Sanarwar, wadda Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanya wa hannu, ta jaddada cewa gwamnati ba za ta yi wasa da tsaro ba, duk da ƙoƙarinta na kare al’adun Kano.
A ƙarshe, gwamnati ta taya al’ummar Musulmi murnar Sallah tare da fatan zaman lafiya da nasara a duk faɗin jihar.