Dsp Barau jibrin ya karɓi kwamitin IGP, kan kafa yan sadan jahohi
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya karɓi mambobin kwamitin jagoranci na Nigeria Police Force a wata ziyarar girmamawa. An kafa kwamitin ne domin samar da tsarin kafa ‘yan sandan jihohi.
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya ƙaddamar da kwamitin mai mambobi takwas a ranar 4 ga Maris, 2026, domin tsara yadda za a aiwatar da tsarin ‘yan sandan jihohi.
Sanata Barau, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin Majalisar Dattawa na duba kundin tsarin mulki na 1999, ya karɓi kwamitin ƙarƙashin jagorancin Farfesa Olu Ogunsakin a Abuja ranar Talata.
A cewar sanarwar mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Majalisar, Ismail Mudashir,
Farfesa Ogunsakin ya yi wa Sanata Barau bayani kan aikin da aka ɗora wa kwamitin, tare da neman shawarwari da gudunmawar Majalisar Dattawa domin ƙarfafa rahotonsu.
Da yake mayar da martani, Barau ya yabawa Sufeto Janar Olatunji Disu bisa aiki tare da shirin Renewed Hope Agenda na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin tabbatar da tsaron ƙasa.
Ya kuma umarci mambobin kwamitin da su mai da hankali kan:
Samar da hanyoyin tabbatar da gaskiya da riƙon amana
Kariya daga amfani da iko ba daidai ba
Wayar da kan jama’a
Ya ƙara da cewa dole ne a gina tsarin da zai ƙarfafa tsaron jama’a tare da rage fargabar ‘yan ƙasa.
Barau ya tuna cewa a lokacin sauraron ra’ayoyin jama’a kan gyaran kundin tsarin mulki na 1999, ‘yan Najeriya sun nuna damuwa da tsoron kafa ‘yan sandan jihohi, don haka dole ne a samar da tsarin da zai kwantar musu da hankali.
Ɗaya daga cikin kudurorin da ke gaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki shi ne wanda ke neman a ba da dama a kafa ‘yan sandan jihohi da na al’umma, domin ƙarfafa tsaron cikin gida da haɗin gwiwar al’umma ta hanyar tsarin doka mai ƙarfi.
Domin tabbatar da haɗin kai da ba kowa dama, kwamitin ya gudanar da tarukan jin ra’ayin jama’a a yankuna shida na ƙasar, inda aka bai wa masu ruwa da tsaki damar bayar da gudunmawa.