Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, yace hukumomin tsaron nigeria suna aiki ba dare ba rana domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa,
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa hukumomin tsaro suna aiki dare da rana domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, tare da ɗaukar matakai masu ƙarfi don inganta tsaro a ƙasar.
Idris ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, inda ya yi bayani kan rawar da hukumomin leƙen asiri ke takawa bayan ƙalubalen tsaro na baya-bayan nan, ciki har da harin da ya faru a Maiduguri.
Ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim, ministan ya yi watsi da zargin cewa hukumomin tsaro sun gaza.
Ya ce:
“Ba na ganin sun gaza. Ina ganin dai akwai buƙatar ƙarin aiki. Hukumomin tsaron Najeriya suna aiki dare da rana domin tabbatar da cewa irin wannan lamari bai sake faruwa ba.”
Ya kuma ƙara da cewa, an samu gagarumin ci gaba wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Maiduguri cikin ‘yan shekarun nan.
Ministan ya jaddada cewa gwamnati tana bai wa harkar tsaro muhimmanci sosai, inda ya ce manufofin gyaran da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na nufin tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya da kuma hana sake aukuwar irin wadannan hare-hare.
Game da batutuwan duniya, musamman rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya, Idris ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, musamman a fannin makamashi.
Ya ce:
“Najeriya a shirye take koyaushe ta taimaka wajen tabbatar da tsaron makamashi a duniya. Duk abin da za mu iya yi don rage tashin hankali, za mu yi. Duniya na buƙatar mai, kuma Najeriya na nan.”
Haka kuma, ya yi magana kan ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi a ƙasashen waje, inda ya ce wannan ziyara na da muhimmanci wajen ƙarfafa dangantakar diflomasiyya, musamman tsakanin Nigeria da United Kingdom.
A ƙarshe, Idris ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare, ƙarfafa tsaro, da kuma tabbatar da cewa ‘yan ƙasa na rayuwa cikin aminci, tare da sanya Najeriya ta kasance ƙasa mai daraja a idon duniya.